Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce takardun sa hannun hukuncin ya rataye Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Abduljabbar kawai yake jira. Inji AminiyaÂ
Wata kotun musulunci ce da ke zamanta a Kano ta zartar da hukuncin kan zargin Malamin da batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotun Kofar Kudu da ke birnin Kano.
Tun da farko Mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya ce ya gamsu da shaida da hujojjin da aka gabatar masa game da karar da ake yi wa Abduljabbar na yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.
Ya ce hujojji sun bayyana cewar Abduljabbar ne ya kirkiro dukkanin wadannan kalamai a cikin karatunsa.
Don haka kotun ta same shi da laifin aikata aifin da ake tuhumarsa da shi wanda aka shafe watanni 15 ana shari’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp