Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani kan nasarar da jam’iyyarsu ta samu a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke jihar Kano.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kotun ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano na ranar 18, ga watan Maris 2023, ta kuma kori Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar (NNPP).
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara
Gwamna Ganduje wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya ce, bai yi mamakin hukuncin ba domin ya riga ya san abin da ya faru a lokacin zabe.
“Ban yi mamaki ba domin duk mun ga abin da ya faru a lokacin zaben. Na biyu, jama’a sun yi ta yi wa jam’iyyar mu addu’a don neman taimakon Allah, don a dawo mana da kujerarmu.” Cewar Ganduje.
Dangane da matakin da NNPP ta dauka na zuwa daukaka kara, Ganduje ya ce ita ce damar da dimokuradiyya ta bayar.
“Wannan wani tanadi ne na doka, idan ba ku gamsu ba ku daukaka kara. Babu laifi a kan hakan. Tsarin kasa ya tanadi daukaka kara. Za mu hadu a can mutane suna yi mana addu’a.
“Ba mu da tsoro, mun yi imani da Allah, kuma duk wanda ya yi imani da Allah zai samu nasara da yardar Allah,” in ji shi.
Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da addu’o’in zaman lafiya da ci gaba, inda ya ce tuni sun aza harsashin ayyukan ci gaba a jihar da za su sanya a gaba.
“Muna godiya ga mutanen jihar Kano da kuma ba su tabbacin cewa mun samu kokensu kuma za mu yi kokarin magance su. Muna gode musu saboda ba da hakuri da suka yi a wannan lokacin.