Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani mai zafi ga Buba Galadima bisa kalaman da ya yi na cewa Ganduje ya rasa tasirin siyasa.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala, ya fitar, Ganduje ya bayyana Galadima a matsayin “ɗan siyasa da ya mutu, aka yi watsi da shi, kuma yana cikin fargaba” wanda ba shi da wani tasiri a siyasar Nijeriya.
- Hisbah A Katsina Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Budurwa A Wani Faifan Bidiyo
- Sin: Matakin Harajin Kwastam Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne
Okpala ya ce Galadima ba shi da kwarjini, kuma yana da tarihin sauya ra’ayi akai-akai don amfanin kansa.
Ya tunatar da jama’a cewa Galadima ya kasance cikin tawagar Buhari a baya amma ya kasa taimaka mata wajen cin zaɓe a lokacin.
Ya yaba wa nasarorin Ganduje a lokacin da yake gwamnan Jihar Kano, yana mai cewa ayyukansa har yanzu suna bayyana kuma yana da farin jini a tsakanin al’umma.
Haka kuma, ya soki jam’iyyar Galadima wato NNPP, yana mai cewa tana cike da rikice-rikice, saɓanin APC a ƙarƙashin shugabancin Ganduje wadda ke tafiya cikin daidaito.
Okpala ya kammala da cewa Ganduje ya mayar da hankali wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba, kuma ba zai tsaya sauraren “maganganun marasa tasiri” kamar na Galadima ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp