Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai mika ayyukan jihar a hukumance ga zababben gwamnan, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida mai barin gado, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa za a gabatar da taron ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Lahadi 28 ga watan Mayu a fadar Gwamnatin Kano.
Malam Muhammad Garba Ya ce tuni kwamitin mika mulki ya sanar da kwamitin karbar mulki na zaɓaɓɓen Gwamna akan al’amarin.
Garba ya ce kwamitocin biyu sun zauna kuma kwamitin mika mulki ya gabatar da takardun mika mulki ga kwamitin karbar mulki, kuma dukkannin bangarorin sun amince da tsare tsaren yadda mika mulkin zai kasance.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Ganduje zai yi fitar karshe daga fadar Gwamnatin Kano a daren yau da zaran an kammala taron mika mulkin, kuma nan take zai bar Kano zuwa birnin tarayya Abuja domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Garba ya ce zai yi hakan ne domin kauce wa rufe filin tashi da sauka na Nnamdi Azikwe da za a rufe shi a daren yau sakamakon bikin rantsuwar da za a yi.
A gobe ne dai za a rantsar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon Gwamnan Jihar Kano a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano