ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 months ago
Annabi

Assalamu alaikum, masu karatu, barkanmu da sake haɗuwa a wannan makon. Za mu ƙarasa batun aure da muke yi kafin daga bisani mu ɗora da wani darasin.

Kamar yadda muka yi bayani a makon da ya gabata, wata rana, Annabi Dawud, yana cikin ɗakinsa yana Ibada, sai ga Mutane biyu sun shigo ba tare da masu gadinsa sun sani ba, sai ya razana, ya ce musu ku kuma su waye kuma daga ina, sai ɗaya ya ce “wannan ɗan’uwana ne, yana da shanu 99, ni kuma ina da ɗaya, amma ya matsa min sai na ba shi ita, dole na ba shi ita sabida ya rinjaye ni a zance ”, bayan Annabi Dawudu ya yi musu hukunci ya tabbatar da cewa mai 99 ya zalumci mai ɗaya sai suka koma.

Nan take, Annabi Dawuda ya fahimci cewa, ya yi wa kansa hukunci ne, sai ya nemi tuba kuma Allah ya gafarta masa.

ADVERTISEMENT

An karɓa daga Hadisin Sayyadina Anas, Annabi (SAW) yana cewa, “Allah ya fifita ni a cikin mutane da abu Huɗu: 1- Na fi kowa kyauta 2- Na fi kowa sadaukantaka 3- Na fi kowa saduwa da Iyali 4- Na fi kowa iya damƙa.”

Manzon Allah (SAW) ya fi kowa haƙuri amma in ka taɓo Allah, za ka gane ya fi kowa iya kai hari. Wata rana Annabi (SAW) ya kai hari ƙabilar Khaibara, sai ga Annabi (SAW) yana cewa, ‘Allahu Akbar, Karibat khaibara’ Khaibara ta rushe. Duk ƙabilar da muka wayi gari a cikinta, za ta yi mummunar Asuba.

LABARAI MASU NASABA

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

Amma alfarma ko matsayi, abun alfahari ne da yabo ga masu hankali a al’adar Mutane, a ce wane, Shugaban ƙasa ne, Gwamna ne, Sarki ne, ko wani Shugabanci dai na daban, alfarmar mutum gwargwadon girmansa a zuciya. Da yawa a kan haɗa shugaba da waninsa a ɗakin kwanciya yayin gabatar da aikin Hajji, amma duk ba su san juna ba, yayin da aka gaya masa cewa, abokin kwananka sarki ne ko shugaba sai ka ga girmansa a zuciyarka ya canza saɓanin a ce ba shugaba ba ne.

Allah tabaraka wa ta’ala ya faɗa cikin girmama Annabi Isah (AS), da faɗinsa “…Wajihan fid dunya wal akhira, ma’ana Mai girma ne a duniya da lahira”

Sai dai, girma ko matsayi mai cutarwa ne daga tulin jama’a, wani yana amfani da damar ya taimaki tulin Jama’a wani kuma ya azabtar da mutane da matsayin. Sabida haka, wanda ya ƙi shugabanci, ya samu hujjah a Shari’a amma in za ka amfana ka amfanar, samun matsayin shi ya fi ɗaukaka.

Annabi (SAW), Allah ya ba shi girma da ɗaukaka na a dinga ganin girmansa da darajarsa a zuciya tun kafin Annabta, lokacin jahiliyya da bayan Annabta.

Da yawan lokuta, Kafiran Makkah suna ƙoƙarin cutar da Annabi (SAW) da Sahabbansa a bayan idonsa amma da sun haɗu da Annabi (SAW) sai su girmama lamarin sa, ba za su iya cutar da shi ba.

Wannan Alhamdu lillah, gadon Annabi (SAW) ne ya bai wa duk masu gaskiya, in ka tsaya wa gaskiya, kullum azzalumai za su yi ta shirin cutar da kai amma in kun haɗu ba za su iya ba sai dai su yi ta shiri a bayan idonka.

Hadisai da misalai na hana Azzalumai cutar da Annabi in sun haɗu suna da yawa, amma za mu zo muku da wasu daga cikinsu.

Sayyidina Ali yana cewa, idan Mutum ya haɗu da Annabi (SAW) a hanya bai san da zuwansa ba, to sai ya razana da yin makerketa sabida ganin sa.

An ruwaito daga wata sahabiya da ake kira Ƙailatu, yayin da taga Annabi (SAW) sai ta razana ta fara makerketa, sai Annabi (SAW) ya ce mata, “ya ke baiwar Allah, ki nutsu, ni ba kowa ba ne sai ɗan mace, mai cin kilishi a Makkah.”

A wani hadisin Abi Mas’ud an ruwaito yana cewa “An kawo wani mutumi gaban Annabi (SAW) yana ta makerketa, sai ya ce masa, sauwaƙe wa kanka Malam, ni fa ba sarki ba ne…” Amma duk wannan girmamawa ce da ƙanƙan da kai na Annabi (SAW), don shi ne cikamakon Manzonni, Allah ya ba shi karamci da kwarjini a duniya da lahira.

Alhamdu lillah! Wannan babin da muka kammala ya yi nazari kan abubuwan da ake alfahari da ƙarantasu a rayuwa kamar bacci da yawan cin abinci sannan ya yi Nazari a kan abinda ake alfahari da yawaita su, kamar auratayya da ɗaukaka. Duk wanda aka ce masa mai yawan bacci da cin abinci ne, an zage shi! Duk wanda aka ce masa yana da yawan ƴaƴa da mata, an yabe shi, sai dai in ba shi da halin kula da tarbiyyarsu da ciyar da su.

Annabi
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

MASU ALAKA

Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani
Dausayin Musulunci

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
SAW
Dausayin Musulunci

Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

October 16, 2026
SAW
Dausayin Musulunci

Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)

October 2, 2026
Next Post
Annabi

Amarya Ta Zuba Wa Mijinta Guba Bayan Kwanaki 40 Da Aurensu

LABARAI MASU NASABA

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

Sun Haifar Da Yunwa Da Talauci A Nijeriya, Muna Ƙoƙarin Kawar Da Su – Tinubu

October 24, 2026
Ya Kamata A Baiwa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa Damar Sauraro

Ya Kamata A Baiwa Muryoyin Kasashe Masu Tasowa Damar Sauraro

October 24, 2026
Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

Mafarauta Sun Kashe Ƴan Bindiga 14, Sun Kuɓutar Da Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

October 24, 2026
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Taraba, Sun Kwashi Kayan Abinci

October 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Kashe Tiriliyan 2.3 Kan Gangamin APC

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.