Da alamu idon Amurka ya rufe a kokarinta na ba kanta fifiko da sanya moriyarta gaba da komai, ta hanyar kakaba haraje-haraje maras tushe kan kasashen duniya, ciki har da kasashe marasa karfi dake bukatar tallafinta a matsayin mai kiran kanta da “babbar kasa”. Matakin kakaba harajin ramuwar gayya da Amurka ke dauka sun kara bayyana ra’ayinta na son kai da neman samun nasara daga faduwar sauran kasashe, lamarin da ya sa na fara tunanin, shin Amurka ta taba damuwa da moriyar sauran kasashe kuwa? Shin ikirarin da take na rajin kare ‘yanci da hakkoki a kasashen duniya gaskiya ne?
A yau Talata kasar Sin ta sanar da cewa muddin Amurka ta aiwatar da barazanarta na kara harajin kaso 50%, to za ta dauki matakin ramuwar gayya ba tare da wata-wata ba don kare muradunta. Ba kasar Sin kadai ba, ina da yakinin sauran kasashe ma za su dauki matakin ramuwar gayya a kan Amurka. Kuma idan aka ci gaba da daukar matakan ramuwar gayya, shin wani alfanu za a samu? ita Amurkar za ta samu fifikon da take buri?
- Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
- Jam’iyyar Labour Ta Yi Barazanar Dakatar Da Peter Obi Da Gwamna Otti
A ganina, Amurka ta yi kuskure na nacewa ga aiwatar da matakan kakaba haraje-haraje maras tushe, domin maimakon samun nasara, asara ce za ta biyo baya. Su kuma wadanda take matsawa, za su farka, su lalaubo hanyoyin kaucewa dogaro da ita. Matakin da take dauka sun fito da rauninta karara, da matsalolin da take fama da su, da kuma nunawa duniya cewa, ita ba abar yadda ba ce domin tana iya yin amai ta lashe muddun tana ganin za ta samu nasara. Wannan kadai ya isa zama gargadi ga kasashen duniya na su tashi tsaye su yaki matakan na son kai, kamar yadda Sin ta yi, kuma su hada hannu wajen lalubo hanyoyin kaucewa mummunan tasirin matakin a kansu ta hanyar kara inganta huldar cinikayya a tsakaninsu da kiyaye ka’idojin tafiyar da kasuwanci da na hulda da kasa da kasa.
Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai.
Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma za a ci gaba da kyautata musu muhallin raya harkokinsu ba tare da ana tufka da warwara ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp