Jama’a da dama ne suka tarbi wani shugaban masu garkuwa da mutane, Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, yayin da ya iso zuwa mahaifarsa da ke Ibbi jihar Taraba, a ranar Lahadi.
Wadume, wanda jami’an rundunar ‘yansandan farin kaya ta ‘Intelligence Response Team’ da ke karkashin kulawar Babban sufeton ‘yansanda suka kama shi a shekarar 2019, an sake shi daga gidan yarin Kuje ne da ke Abuja, a ranar Juma’a, kamar yadda majiya ta bayyana.
- 2023: Manyan Jiragen Ruwa 75,000 Suka Yi Hada-hada A Tashar Lekki
- Karin Kudin Hajji: Gwamna Inuwa Ya Tallafa Wa Maniyyatan Gombe Da Naira 500,000 Kowanne
Majiyar gidan yarin ta shaida wa Daily Trust cewa, Wadume ya kammala hukuncin daurin da aka yanke masa ne a gidan yarin.
Jaridar ta rahoto cewa, dimbin jama’a ne da suka hada da matarsa da sauran jama’a ne suka tarbe shi a kogin Benuwai kan hanyarsa ta zuwa garin Ibbi inda mahaifarsa ta ke.
Wani mazaunin garin Ibbi mai suna Musa Garba ya ce, garin ya tsaya cak yana tsumayin isowar Wadume.