Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da bada tallafin Naira 500,000 ga kowane mahajjacin jihar daga cikin maniyata 1,373 da za su yi aikin Hajjin bana.
Amincewar ta zo ne biyo bayan sanarwar da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta fitar a baya-bayan nan game da sauye-sauyen da aka samu a kudin Hajjin bana.
- Zaben Edo Da Ondo: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gana Da Hukumar Zabe
- Hajjin 2024: An Bukaci NAHCON Da Jihohi Su Bayyana Alawus Na Tafiyar Alhazai
Inuwa Yahaya ya ce an bada tallafin ne don ragewa maniyata radadin kalubalen halin da suka tsinci kansu biyo bayan karin kudin hajjin bana.
Wannna bayanin dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya fitar ga manema labarai.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi fatan wannan tallafi zai taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin bana cikin tsanaki, tare da inganta jin dadin maniyyatan Jihar Gombe dama samar musu yanayi mai kyau na gudanar da ayyukan addini duk da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi.