A ranar Lahadin satin da ya gabata ne aka kammala wasannin Nakasassu da ya hada ‘yan wasa daga sassa daban-daban na Duniya kamar yadda aka kammala na masu lafiya a watan da ya gabata a kasar ta Faransa.
Sai dai daman tun farko hukumomin Birnin na Paris sun yi alkawarin gudanar da gasar da za a dade ana tuna ta yayin da suke shirin karbar bakuncin gasar Olympics ta Nakasassu ta wannan shekara ta 2024.
- Sakon Da Aka Isar Game Da Yanayin Tekun Kudancin Kasar Sin Daga Wasu Taruka Uku
- Lallai Ƴan Nijeriya Suke Bibiyar Aiyukan Ƴan Majalisu – Shugaban EFCC
Bayan da aka yi gasar wasannin Tokyo a 2021 ba tare da ‘yan kallo ba saboda Annobar Korona, sannan ita kuma gasar Rio ta 2016 ta gamu da matsalollin kudi , Birnin Paris ya kasance cikin matsin lamba kan ya gudanar da gasar da za ta kasance daidai da wadda aka yi a Birnin Landan a 2012 ko ma gasar ta Paris ta zarta ta.
Bikin bude gasar da za a ranar Larabar da ta gabata da karfe 7:00 na yamma agogon
Nijeriya zai kasance ne a ‘Place de la Concorde’, inda za a bayar da kyaututtuka na lambobin Zinare 549 ga ‘yan wasan da suka yi bajinta a washegari.
Sannan an kammala gasar inda aka yi bikin rufewa a filin wasa na Stade de France ranr Lahadi 8 ga watan Satumba 2024, sannan an sayar da tikiti kusan miliyn biyu na shiga gasar zuwa yanzu, inda kuma har yanzu akwai 500,000 da ba a saya ba. Bayan irin nasarar da aka samu ta gasar Olympics da aka kammala a Paris hukumomin birnin sun ce wannan somin-tabi ne.
Gasar ta Paris ta samu ‘yan wasa mata da tawagogin ‘yan wasa da ba a taba samu ba a wata gasa ta Nakasassu ta Olympics, sannan kuma za a nuna a tashoshin talabijin a yankuna da dama masu yawan da ba a taba yi ba a baya.
Kuma Faransa ba ta taba karbar bakuncin wasannin Nakasassu na bazara ba, koda yake ta karbi bakuncin wasannin lokacin hunturu na 1992 da aka yi a Albertbille.
Nijeriya ta kammala wasannin wannan shekarar inda ta kammala a mataki na 40 bayan ta lashe lambar yabo guda bakwai ciki kuwa akwai gwal guda biyu da tagulla guda uku da kuma azurfa guda biyu da aka samu a gasar.
‘Yan wasa irin su Onyinyechi Mark da Folashade Oluwafemiayo da Bose Omolayo da Flora Ugwunwa da Esther Nworgu da sau Ogunkunle su ne suka lashewa Nijeriya wadannan kyaututtukan a wannan shekarar da aka kammala.