Bisa ga dukkan alamu, ci gaban da kasar Sin ta samu a fannoni daban-daban da irin gudummawar da take bayarwa ga ci gaban zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwar tattalin arziki da sauran sassan rayuwa a fadin duniya, ya damu wasu kasashe, wadanda suke kallo kansu a matsayin jagororin duniya.
Wannan ya sa daga lokaci zuwa lokaci, irin wadannan kasashe suke neman bata sunan kasar Sin ko salon jagorancin kasar da al’ummar kasar suka yi na’am da shi ko wani tsari da ta gabatar da nufin inganta rayuwar daukacin bil-Adama, kamar shawarar ziri daya da hanya daya da makamantansu.
A wasu lokuta ma, irin wadannan kasashe dake adawa da ci gaban kasar Sin, kan fake da batutuwan tsarin demokiradiya da hakkin dan-Adam wajen neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.
Sai dai, yanzu kan mage ya waye, kasashe da dama sun fahimci makircin kasashen yamma, inda suka fara dawowa daga rakiyarsu, domin kada su zuba musu kasa a cikin kununsu. Ta hanyar lalata shirye-shirye masu fa’ida da Sin din ta gabatar, da galibin kasashe masu tasowa suka amfana da su.
Na baya-bayan shi ne ministan kudi na kasar Bangladesh, inda ya fito kara ya soki wasu rahotannin karya da kafofin yada labaran Burtaniya suka yi kan kasar Sin, matakin dake nuna irin cikakkiyar amincewa da juna dake tsakanin Sin da Bangladesh, kuma hakan ya tabbatar da abin da kasar Sin ta sha fada cewa, gaskiya ba ta buya, kuma komin dadewa, adalci zai bayyana kansa.
A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, har kullum kasar Sin tana tare da sauran kasashe masu tasowa, kana tana gudanar da hadin gwiwar “ziri daya da hanya daya” da masu neman hana ruwa gudu ke neman batawa bisa tsarin tuntubar juna, da gudummawar hadin gwiwa, da samun moriyar juna.
Bayanai sun tabbatar da cewa, batun “tarkon bashi na kasar Sin” a zahiri wani “tarkon tattaunawa ne” da wasu mutane masu mugun nufi suka kirkira, don kawo cikas da kuma gurgunta hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa.
Amma yanzu kan gaskiya ta bayyana, babu wanda zai rudi kasashen da suka amfana da tallafi da goyon bayan da kasar Sin ke baiwa abokanta kasashe masu tasowa.
Sanin kowa ne cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, ta samu gagarumin goyon baya da shigar kasashe masu tasowa da dama.
Haka kuma hadin gwiwar ta haifar da kyakkyawan sakamako, ta kuma samar da fa’ida ta hakika ga jama’ar dukkan kasashe.
Don haka, duk wasu kalamai marasa kyau da ke neman bata sunan shawarar da hadin gwiwar Sin da sauran kasashe masu tasowa, da masu neman mayar da hannu agogo baya ke kirkira, kaikayi ne zai koma kan mashekiya. (Ibrahim Yaya)