Gwamnatin Trump a kwanakin baya ta sanar da rufe hukumar kula da harkokin raya kasa da kasa ta USAID, matakin da ya kasance tamkar ja-in-ja a tsakanin jam’iyyun siyasa na kasar, sai dai hakan ya ta da hankalin wasu kafofin yada labarai da ma kungiyoyin da suka bayyana kansu a matsayin wai “masu zaman kansu”, har ma ya tona mana asirin USAID na fakewa da sunan samar da gudummawa domin amfani da kafafen yada labarai wajen cimma muradunta.
Bethany Allen-Ebrahimian tana aiki da cibiyar nazarin manufofin tsare-tsare na kasar Australia(ASPI), wadda ta sha yada karairayi na shafa wa kasar Sin bakin fenti ta kafofin yada labarai na kasashen yamma. A wata mukalar da ta wallafa a shafin cibiyar ASPI, a bayane ta ce, kungiyoyin NGO da suka samar mata bayanan shafa wa kasar Sin kashin kaza, har da tsarin da kungiyoyin suka kafa na kin jinin kasar Sin, sun dogara ne da kudaden da gwamnatin Amurka ta samar musu. Ta kara da cewa, muddin dai gwamnatin Amurka za ta ci gaba da samar da kudade ga kungiyoyin, to, za ta iya ci gaba da samar da labarai na bata sunan kasar Sin a fadin duniya, a kokarin kare “dimokuradiyya da ‘yanci” da ma “hakkin dan Adam”. Sai dai ba ta yi zaton abin da ya faru bayan da ta wallafa mukalar a shafinta na sada zumunta ba, inda masu bibbiyar shafinta da dama suka gano cewa, ashe su wadannan mutane suna karbar kudade ne don shafa wa kasar Sin kashin kaza, ke nan ya ya za a samu kamshin gaskiyar abubuwan da suka fada? Wasu kuma sun ce, ba za a gano alakar “’yanci da dimokuradiyya da hakkin dan Adam” da wadanda ke karbar kudin gwamnatin Amurka domin tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin da lalata tsaronta da ikon mulkin kanta ba, a maimakon hakan, matakin ya kara tabbatar da yadda kungiyoyin leken asiri na kasar Amurka ke amfani da USAID wajen hambarar da gwamnatocin wasu kasashe.
- Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sace Iyali 3 A Filato
- Kasafin 2025: Kar A Yi Sakaci Macizai Da Birai Su Haɗiye Dala Biliyan 1.07 Da Aka Ware Wa Kiwon Lafiya – Atiku
Kungiyar Reporters Without Borders ma ta damu matuka da matakin gwamnatin Amurka na rufe USAID. Reporters Without Borders kungiya ce ta kasashen yamma wadda ta kan fake da sunan wai “’yancin labarai” da “rahotanni masu zaman kansu” wajen tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe. A wani rahoton da ta bayar mai taken “Yadda Trump ya dakatar da samar da kudade ga USAID ya jefa ayyukan labarai na duniya cikin rudani”, ta ce, Yadda Trump ya dakatar da samar da kudade ga USAID na yin tasiri ga ‘yan jarida masu zaman kansu da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ke kasashen Iran da Rasha.” Lallai abin mamaki ne yadda suke karbar kudaden gwamnatin Amurka amma kuma suke bayyana kansu a matsayin masu zaman kansu.
Rashin kunya ne yadda Amurka ta dauki irin wadannan munanan matakai na sayen kafafen yada labarai, amma kuma ya kamata mu yi hankali da manufar da take neman cimmawa. Dalilin da ya sa Amurka ke zuba kudade tana sayen ‘yan jarida shi ne, tana bukatar kafofin yada labarai su taimaka mata wajen cimma burinta, ko wajen neman tsoma baki a harkokin wasu ko kuma don wanke kanta daga laifuffukan da ta aikata.
A ‘yan shekarun baya, yayin da kasar Sin ke dada bunkasa, ita Amurka ta yi kuskure har ta dauki kasar Sin a matsayin babbar abokiyar takararta, lamarin da ya sa ta dauki matakan dakile kasar Sin daga dukkan fannoni, ciki har da fannin yada labarai. Musamman ma a yayin da Sin da kasashen Afirka suka yi ta inganta hadin gwiwarsu, har kuma aka aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata, tattalin arzikin kasashen da abin ya shafa ya yi ta bunkasa, kuma manyan ababen more rayuwa da ma rayuwar al’ummar kasashen ma sun kyautata. Amma Amurka wadda ta dade tana nuna fin karfi a duniya ba ta ji dadin hakan ba, don haka ma muke ta kara karanta rahotanni da ke shafar “sabon salon mulkin mallaka” da “tarkon bashi” da “barazana daga kasar Sin” daga wasu kafofin yada labarai.
Sai dai yadda gwamnatin Trump ta sanar da rufe USAID ya ba da damar tona asirinta, kuma tabbas tarihi zai tabbatar da cewa, gaskiya na hannun wadanda ke kokarin samar da ci gaba da kiyaye hadin gwiwar cin moriyar juna da ma wadanda ke kokarin tabbatar da makomar dan Adam ta bai daya.