• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gaskiyar Danniyar Amurka

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

A ranar 19 ga wata, agogon wuri, wasu masu adawa da yake-yake na kasar Amurka sun yi gangami a birnin Washington na kasar, inda suka bukaci Amurka da ta dakatar da taimakawa kasar Ukraine ta fuskar aikin soja, tare da yin kira da a wargaza kungiyar tsaro ta NATO.

Duk da haka kwana guda bayan gangamin, wato jiya Litinin 20 ga wata, shugaba Joe Biden na Amurka ya kai wata ziyarar ba-zata zuwa Ukraine, inda ya sanar da kara bai wa Ukraine taimakon dalar Amurka miliyan 500, ciki had da makamai.

  • Wang Yi Ya Yi Kwarya Kwaryar Ganawa Da Antony Blinken Na Amurka

Lamarin da ya nuna cewa, Amurka ita ce da ke da hannu wajen rura wutar rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine cikin shekara guda da ta gabata, wadda kuma ta fi yin danniya a duniya yanzu.

Rura wutar rikicin Ukraine, wani bangare ne na yunkurin Amurka na yin danniya a duniya a shekarun baya-bayan nan. Rahoton “yadda Amurka ke yin danniya da kuma illolinsa” da kasar Sin ta fitar jiya Litinin ya bayyana gaskiyar danniyar Amurka a fannonin siyasa, aikin soja, tattalin arziki, kimiyya da fasaha, da al’adu. Rahoton ya yi wa kasashen duniya karin bayani kan yadda Amurka take yin danniya a duniya da abubuwa na rashin kunya da take yi.

Daga tunzura a yi mulkin danniya a kasashen Turai da Asiya, zuwa kulla makarkashiyar yin juyin mulki a yammacin Asiya da arewacin Afirka, kullum Amurka tana yunkurin kafa tsari da oda a wasu kasashe da ma duniya baki daya, da sunan shimfida demokuradiyya da kiyaye hakkin dan Adam, amma hakika ba a samu demokuradiyya a wadannan yankuna da kasashe ba, sai tashin hankali da bala’u kawai. Demokuradiyya irin ta Amurka ba ta samu nasara ba.

LABARAI MASU NASABA

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

Kullum Amurka tana sadaukar da tsaron wasu kasashe, dakile ci gaban wasu kasashe, da sadaukar da alherin al’ummun wasu kasashe, don neman yin danniya, da kiyaye yadda take yi, da kuma yin amfani da fifikonta. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera
Daga Birnin Sin

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

October 22, 2025
Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
Daga Birnin Sin

Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

October 22, 2025
Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

October 22, 2025
Next Post
NRC Ta Dakatar Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa A Nijeriya Zuwa Bayan Zaben Shugaban Kasa

NRC Ta Dakatar Da Zirga-Zirgar Jiragen Kasa A Nijeriya Zuwa Bayan Zaben Shugaban Kasa

LABARAI MASU NASABA

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera

October 22, 2025
An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Na Bana

October 22, 2025
Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana

October 22, 2025
Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

Tinubu Ya Amince Da Tallafin Naira 250,000 Ga Ƙananan ’Yan Kasuwa A Jihar Katsina

October 22, 2025
Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

Kasar Sin Ta Sake Farfado Da Muhimman Koguna Da Tafkuna 88 A Kokarin Inganta Muhalli

October 22, 2025
Tanka

Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja

October 22, 2025
Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

October 22, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

October 22, 2025
Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.