A yayin da ake dab da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakan Isra’ila da Hamaz a yankin Gaza, Jakadan Faladinawa a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya bayyana cewa wadanda suka yi shahada a kisan kare-dangi da Isra’ila ke yi a Gaza sun haura mutum 14,000 wanda daga ciki akwai kimanin yara 6,000 da mata akalla 4,000.
Har ila yau, ya kara da cewa akwai Falasdinawa kimanin 6,000 da har yanzu suke karkashin baraguzai baya ga wasu da dama da aka kashe a kan tituna da ba a samu damar kwashe gawarwakinsu ba balle a yi musu jana’iza saboda yanayin da ake ciki.
- Gaza: Isra’ila Ta Kashe Mutum 14,200, Daga Ciki Yara 6,000, Mata 4,000 – Jakadan Falasdin
- Kotu Ta Bayar Da Belin Tsohon Shugaban Hukumar KASCO Kan Miliyan 500
Jakadan wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a Ofishin Jakadancin Falasdin da ke Abuja, ya ce adadin wadanda aka kashe a yankin da Isra’ila ta mamaye a Gabar Yammaci ya haura 200, yana mai cewar, “a yankin gabar yamma musamman a kauyen Huwara da yake fama da hare-haren zalunci da kungiyoyin ta’addanci na ‘yan share wuri zauna suke kaiwa, daga cikin shaguna da sauran wuraren kasuwanci 300 da ake da su, guda 45 ne kawai aka bari su bude, sauran kuma sojoji sun rufe. Wannan karin asara ce ga rugurgujajjen tattalin arzikin Falasdin.”
Abu Shawesh ya kuma bayyana cewa, Isra’ila ta gaza kawo kwakkwarar shaida ko guda daya game da zargin da take yi cewa, ana amfani da asibitoci a matsayin sansanin mayaka duk da tsawon lokacin da ta dauka tana yada karairayi, maimakon haka ma sai ya zama shaidar bogin da take nunawa ya zama abin dariya da yi mata ba’a hatta a kafafen sada zumunta na kasarta.
Ya yi kira da a kafa kwamitin bincike sahihi da zai tantance duk wata shaida da Isra’ila take cewa tana da ita a kan amfani da asibitoci a matsayin sansanin mayaka a Gaza domin tabbatar da gaskiya, yana mai cewar babu lungu da sakon babban asibitin Gaza (Alshifa) da Isra’ilar ba ta sani ba, kamar yadda hakan ya tabbata a bayanin da tsohon Firaministan Isra’ila, Euhd Barak ya yi cewa “tsawon gomman shekaru su suke gudanar da wurin (asibitin)… mu muka taimaka musu suka gina wadannan wuraren na karkashin kasa domin samar da karin wurin aiki a dan kankanin ginin asibitin.”
Jakadan ya kuma nunar da cewa babbar muguwar aniyar da Isra’ila take da ita a kan ta’addancin da take yi ita ce tarwatsa duk wasu kayayyakin more rayuwa da ke Gaza, “domin ya zama mutane ba za su iya rayuwa a yankin ba, ko da bayan yakin”.
Ya nuna takaicin yadda duk da rashin kwakkwarar shaida, amma kasashen turawan yamma da dama tare da kafafen yada labarunsu har yanzu suke nuna goyon baya ga Isra’ila tare da ci gaba da nanata karairayinta.
Hakazalika, Abu Shawesh ya bayar da misalai daga bayanan da hukumomin Majlisar Dinkin Duniya daban-daban suka yi game da ta’asar da Isra’ila take tafkawa, yana mai cewar, “UNRWA ta ayyana cewa, sama da mutum miliyan 1.6 daga cikin miliyan 2.2 suka rasa gidajensu. Wannan shi ne mafi muni tun daga 1948. Yanayin barnar da ake yi na da matukar tayar da hankali. An ruguza unguwanni gaba daya. Akalla makarantun UNRWA 154 da sauran wasu gine-gine duk an mayar da su matsuguni, inda mutum 810,000 ke rayuwa a ciki.”
Jakadan ya nuna takaici da irin halin da aka jefa mata da yara da sauran masu rauni da yakin ya shafa, yana mai jaddada yadda hakan ke shafar lafiyar kwakwalensu.
“Kwana uku da suka gabata, ranar 20 ga Nuwambar 2023, an yi bikin ranar ‘yancin yara ta duniya. To, muna so mu tunatar da masu rajin kare ‘yancin yara cewa, a yayin da ake kashe yaran Falasdinawa a kullu yaumin babu kakkautawa na tsawon kwana 45 me suka yi? Sun yi gum da bakinsu, har ma da ba da kariya ga wadanda suke wannan aika-aika na kisan kiyashi.”
Bugu da kari, Jakadan na Falasdin ya ce bisa bayanin da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Turai da Yankin Mediterranean ta yi, “Isra’ila ta jefa bama-baman da suka kai nauyin ton 2,500 a Gaza wanda hakan ya yi daidai da karfin bam na Nukiliya guda biyu, daga ranar da ta fara kai hare-hare a Gaza. Karfin bama-baman sun haura na wanda aka jefa wa Hiroshima na Japan. Hiroshima ta kai fadin kilomita 900 amma Gaza ba ta wuce fadin kilomita 360 ba. Isra’ila tana amfani da bama-bamai masu muguwar barna, wasu ma nauyinsu ya kai kilogiram 150 zuwa 1000, wannan daga bayanan Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Galant aka ji lokacin da ya ce an jefa fiye bama-bamai 10,000 a Gaza kawai, yana mai cewar yankin da aka yi abin bai wuce fadin kilomita 56 ba.”
Jakadan ya ce, kamar yadda hukumar ta fada, an riga an tattara bayanan yadda Isra’ila ta yi amfani da abubuwan da aka hana amfani da su a duniya ciki har da bama-bamai masu kwasfa da sinadaran guba masu zagwanye naman jiki.
“Haka nan kuma, a sakamakon gwale-gwale da ukubar da ake wa daurarrun Falasdinawa a gidajen yarin Isra’ila, an kashe mutum biyar, su ne: Omar Daraghmeh (mai shekara 58), Arafat Hamdan (dan shekara 25), Majed Zaqoul (dan shekara 32), Abdel Rahman Mari (dan shekara 33) da kuma Thaer Abu Assab (mai shekara 38).” In ji Jakadan na Falasdin a Nijeriya Abdullah Abu Shawesh.