Yayin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu, ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya yi gargadin cewa, idan har yunkurin diflomasiyya na dakatar da kai hare-hare ta sama da kai farmaki ta kasa a zirin Gaza bai yi nasara ba, to akwai yiwuwar rikicin ya kara rincabewa a kasa shawo kan shi.
Amir-Abdollahian ya nanata cewa, akwai yuwuwar wasu kungiyoyi da ke yankin su tsunduma cikin yakin idan aka kasa taka wa Isra’ila burki, in ji rahoton RT.
- Manufar Kafa Kasashe Biyu Hanya Ce Daya Tilo Ta Warware Rikicin Palesdinu Da Isra’ila
- Wang Yi: Sin Tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Da Lamirin Da Ya Shafi Dan Adam Kan Batun Falasdinu
Hossein Amir-Abdollahian ya shaida wa Al Jazeera a ranar Lahadin da ta gabata cewa, “Idan matakan da aka dauka na dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kananan yara a zirin Gaza ya cutura, to akwai yiwuwar wasu kungiyoyi su shiga cikin yakin.”
Ya kara da cewa, “Idan har Isra’ila ta yanke shawarar shiga Gaza, shugabannin gwagwarmaya (Hamas) za su mayar da ita makabartar ga rundunar sojojin,” in ji shi.
A ziyarar da ya ke yi na diflomasiyya a yankin, ministan na Iran ya gana da wani shugaban siyasa na kungiyar Hamas Ismail Hanieyh a Qatar, inda ya yi kira ga sauran kasashen musulmi da su goyi bayan Falasdinu, ya kuma ba da tabbacin cewa, Iran za ta ci gaba da kokarinta na dakatar da “laifukan yaki da Isra’ila ke aikatawa.”
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ka’idojinta da kimarta wajen goyon bayan al’ummar Falasdinu,” in ji shi.