Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kasa ta kara tsawaita yajin aikin da take yi.
Duk da cewa babu takamammen bayani kan karin wa’adin, kungiyar ta dauki matakin ne bayan kammala zaman taron zartarwar kungiyar ta kasa.
In ba a manta ba a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin neman cika musu alkawarin yarjejeniyarsu da Gwamnatin tarayya wacce bangarorin biyu suka Sanya Wa hannu tun shekarar 2009.
Karamin Ministan Kwadago da Aiki Festus Keyamo, a baya ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta iya cika wannan alkawuran ba na biyan bukatun Kungiyar Malaman Jami’o’in (ASUU) gaba daya.
Sai dai ya bayyana cewa, gwamnati ta yi iya bakin kokarinta, ya kuma yi kira ga iyayen dalibai da su roki ASUU su janye yajin aikin da ‘yaki ci yaki cinyewa’