Bayan shafe shekaru 20 yana a majalisar wakilai, shugaban majalisar Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga mukaminsa.
Gbajabiamila, wanda aka rantsar a matsayin dan majalisar a karo na shida a ranar Talata, ya mika takardar murabus dinsa ga sabon kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, a zauren majalisar a ranar Laraba.
- Dalilin Da Ya Sa Muka Rushe Shataletalen Gidan Gwamnati —Gwamnatin Kano
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Bincike Kan Hatsarin Jirgin Ruwan Kwara
A cikin wasikar, shugaban masu rinjaye na majalisar ya ce hakan ne zai ba shi damar rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da Bola Tinubu ya ba shi.
A ranar Juma’a, 2 ga watan Yuni, 2023 ne shugaba Tinubu ya nada Gbajabimila a matsayin shugaban ma’aikatansa.
An zabe shi a majalisar don wakiltar mazabar tarayya ta Surulere ta 1 da ke Jihar Legas tun a shekarar 2003.
Tsohon dan majalisar ya rike mukamai daban-daban ciki har da mukamin shugaban marasa rinjaye da kuma kakakin majalisar.
Kafin mika takardar murabus din tasa, Gbajbiamila ya gabatar da kudirin farko a zauren majalisa na 10 kan “Bukatar fara daukar matakai don dakile barnar da ambaliyar ruwa ke yi da kuma lalata dukiyoyin jama’a”.