Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya janye kudirinsa ya yin takara a 2027, saboda matasa masu jini a jika su samu daman yin takara.
DUK dai a hukumance Atiku bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a 2027 ba, amma wasu daga cikin masu taimaka masa sun bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasan zai tsaya takara a zabe mai zuwa.
- Shugaban Karamar Hukuma A Kano Ya Yi Murabus, Wani Kuma Ya Fice Daga APC Zuwa NNPP
- Yawan Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Ketare A Bara Ya Karu Kamar Yadda Ya Kamata
George ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da gidan talabijin na Arise, inda ya bayyana cewa Atiku zai cika shekara 18 a 2027, ya tsufa da mulkin Nijeriya.
A cewar jigon jam’iyyar PDP, ya kamata Atiku ya kasance mai mara wa matasan jam’iyyar baya maimakon ya tsaya takara a 2027.
George ya ce, “A yanzu haka dan’uwana Atiku Abubakar yana da shekaru 77, a 2027 kuwa zai kasance yana da shekaru 81. Ya kamata Atiku ya bai wa matasan Nijeriya daman tsayawa takara, domin su ne suke da jini a jika na iya mulkin kasar nan.
“Ya kamata Atiku ya kasance daya daga cikin dattawan kasar nan da za su dunga bayar da shawarwari,” in ji George.