Dabbobi da Gidaje sun ƙone a wata gobara da ta tashi a kauyen Ɗanzago da ke karamar hukumar Ɗanbatta a jihar Kano a ranar Laraba.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce wani Abdurashid Sha’aibu ne ya sanar mata da afkuwar lamarin da misalin karfe 10:48 na safe.
- Xi Jinping Zai Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya Karo Na 9 A Harbin
- Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar ACFO Saminu Yusif Abdullahi ya ce ma’aikatan kashe gobara daga sashin Ɗanbatta sun isa wurin da gobarar ta tashi da misalin karfe 11:22 na safe.
A cewar Abdullahi, da farko gobarar ta lakume wani katafaren gida na Ado Yubai, mai dauke da dakuna 17, da bangarori tara, da kuma wurin ajiyar kayayyakin abinci.
Shanu biyu, tumaki 36, awaki 17, kaji 10, da kuma rumbun ajiyar abinci 19 ne suka ƙone sakamakon mummunar gobarar.
Sai dai jami’an kashe gobara, sun yi nasarar ceto tumaki biyu, da shanu hudu, da rumbun abinci guda biyu, da sauran kayayyaki masu daraja.
Abdullahi ya ci gaba da cewa, daga bisani wutar ta bazu zuwa wani gidan Ibrahim Mai Gariyo, inda ta lalata dakuna, da rumbun ajiyar abinci sannan kuma ta kone tumaki takwas da awaki uku.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp