Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa wani gida da hasalallun matasa su ka kai wa hari a Bauchi, ba na Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ba ne.
Hukumar ta ce ba Yakubu ne ke da gidan ba, a cikin wata sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na shugaban, Rotimi Oyekanmi ya fitar a ranar Asabar.
Jami’in yaɗa labaran ya ce Yakubu ba shi da gida a Bauchi, don haka masu cewa gidan ne, ji-ta-ji-ta ce kawai su ke yaɗawa don su ɓata masa suna.
“Gidan da aka nuno a soshiyal midiya, a cikin wani bidiyo da wasu matasa su ka kai wa hari, ba gidan Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ba ne.
“Shugaban Hukumar Zaɓe ba shi ke da wannan gida da aka nuno ba. Saboda haka bai mallaki wannan gida a Bauchi ko ma a wane gari ba a duniya.
“Danganta gidan da Shugaban INEC ci gaban wata maƙarƙashiya ce da yarfen da ake yi masa, domin su ɓata masa suna kawai. Wannan kuma duk aikin masharranta ne.
“Hukumar Zaɓe da shugaban ta na kira ga jama’a su yi watsi da masu yarfen cewa gidan shugaban hukumar ne aka kai wa hari, a Bauchi.”