Gidauniyar ‘British American Tobacco’ tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara sun raba kajin kiwo ‘yan watanni 5 ga mata 200 domin samar da kwai don bunkasa dorewar tattalin arzikinsu.
Bikin raba kajin ya gudana ne a Cibiyar kiwon kaji, ta Jihar Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.
- Kotu Ta Kori Shugaban KANSIEC Da Wasu Mutane 5 A Kano
- Adadin Man Fetur Da Ake Sha A Nijeriya Ya Ragu
Babban Manajan gidauniyar, Mista Oludare Odusanya da ya samu wakilcin Manajan shirye-shirye na jihar Zamfara Dr. Umar A. Maina ne gabatar da jawabi a madadinsa.
Dakta Maina ya ce, kiwon kaji sana’a ce da za ta kawo sauyi, ba wai kawai samun kudin shiga ba, har ma da inganta samar da abinci da kuma karfafa hadin kan al’umma”.
“Gidauniyar British American Tobacco tun lokacin da aka kafa ta a 2002 tana tallafawa Gwamnatin Tarayya da ta Jihohi a shirye-shiryen bunkasa noma, kuma ta kashe sama da Naira biliyan 4 wajen tallafawa masu karamin karfi a karkara.
A cewarsa, a jihar Zamfara, “shirin ya zabo mata 200, kowacce za ta samu kaji nuwaila guda 20, da buhun abinci na musamman da aka samar da kuma bitamin da za su tallafa wa kiwon kaji dan ingancin lafiyar su.
“Wannan yunƙurin ba kwai ba ne, yana haɓaka tattalin arziƙi a cikin al’ummominmu.”
A nata jawabin, Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa gidauniyar akan Tallafin da ta kawo jihar kuma ta bayar da tabbacin cewa, gwamnatin jihar za ta bayar da tallafin da ake bukata domin dorewar kiwon kajin.