Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar cewa za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba, 2024, duk da hukuncin Kotun Tarayya na hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) gudanar da zaben.
Kotu ta sauke shugabannin KANSIEC da wasu mambobinta saboda alaka da siyasa, amma gwamnatin jihar ta jaddada kudurinta na ci gaba da gudanar da zaben, ko da babu jami’an tsaro.
- Yadda Dortmund Ta Barar Da Garinta A Santiago
- Kasar Sin: Tsohuwar Kasa, Mai Jagorantar Zamanantar Da Duniya
Lawan Hussaini Dala, Shugaban Masu Rinjaye, ya soki hukuncin kotun, inda ya bayyana cewa ya saba da umarnin da Alkalin Kotun Mai Shari’a Nura Ma’aji ya bayar, wanda ya hana jam’iyyun siyasa tsoma baki a harkar zabe.
Dala ya yi nuni da cewa umarnin Kotun Koli ya bukaci jihohi su gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin karshen watsn Oktoba.
KANSIEC ta fuskanci kalubale saboda tsauwala kudin fom din takara, kan Naira miliyan 10 na dan takarar shugabancin karamar hukuma da miliyan biyar ga kansila.
Amma daga bisani ta rage bayan shigar da kara a Kotun Tarayya.
Har ila yau, wata Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarni na hana jam’iyyun siyasa tsoma baki a shirin zaben, wanda ya bai wa KANSIEC damar ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben.