Gidauniyar tallafawa marasa Karfi (IRM) tare da haɗin gwiwar Hukumar Gidauniyar Inshorar Lafiya ta Jihar Kaduna (KADCHMA), ta kaddamar da wani shirin inshorar lafiya kyauta da nufin samar da kulawar lafiya ga mutane 200 daga bangarorin Musulmai da Kiristoci a Jihar Kaduna.
Da yake jawabi a wajen taron, Daraktar tsare- tsare na Gidauniyar, Alhaji Muhammad Inuwa Sabo, ya bayyana cewa shirin zai taimakawa kudirin gwamnatin jihar na samar da ingantacciyar kulawar lafiya ga kowa ba tare da la’akari da addini ko matsayi ba.
- Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
- Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya
Shirin bayar da tallafin lafiyar wanda mai taimakawa gwamnan Kaduna akan harkokin bayar da Agajin Gaggawa, Hon. Ibrahim Rilwanu Muhammad, wanda kuma shi ne shugaban gidauniyar ta IRM ne ya dauki nauyin inshorar lafiya na tsawon shekara guda ga wadanda suka amfana, karkashin tsarin KADCHMA.
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.
Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.”
A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa.
Ya kara da cewa kaddamar da inshorar lafiya kyauta na shekara guda babban ci gaba ne a cikin gyaran fannin lafiya da ake gudanarwa a jihar, inda ya yaba da kokarin gidauniyar IRM wajen tallafawa rayuwar al’ummar Kaduna – Musulmai da Kiristoci.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin daga Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen Kaduna da kuma kungiyar ci gaba ta Darikar Tijjaniyya ta jihar Kaduna sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar da kuma gwamnatin jihar, inda suka ce inshorar lafiya kyauta za ta rage musu nauyin kashe kudin magani tare da karfafa hadin kai a tsakanin al’umma da samar da zaman lafiya.














