• English
  • Business News
Monday, June 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

by Mubarak Umar
3 years ago
in Bakon Marubuci
0
Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Nijeriya, kasa ce da Allah ya hore wa dimbin arziki ta kowanne fanni.

Idan aka duba arewacin kasar, Allah ya albarkace shi da arzikin noma a lokacin damuna da rani, har ila yau, makiyaya su ma na taimakawa matuka wajen bunkasar tattalin arzikin yankin da ma kasar bakidaya, ta hanyar samar da ingantaccen nama, nono, manshanu, takin gargajiya, da sauransu. Sai dai, a ‘yan tsakanin shekarun nan, yankin da aka sani da yalwar arziki, zaman lafiya da walwala, ya tsinci kansa a yanayin tashe-tashen hankula, dalilin rikicin da ya faro tsakanin manoma da makiyaya, wanda daga bisani ya rikide ya koma kan mai uwa da wabi.

  • Me Ya Sa Ba A Fara Shekarar Hijirah Da Ranar Badar Ko Ranar Cikar Wahayi Ba? (I)
  • Nasarar Tsarin CBN Na Samar Da Kudaden Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya

Kididdiga ta nuna cewa Arewacin Nijeriya na yin asarar miliyoyin Naira sakamakon rikicin Fulani da manoma, wanda a yanzu ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, saboda haka akwai bukatar al’umma ta tashi haikan domin magance matsalar ta dukkan hanyar da ta kamata.

A mafi yawancin nazarce-nazarcen da masana tsaro suka yi, sun tafi a kan cewa abun da ya janyo wadannan rikice-rikice, satar mutane da kai hari kauyuka babu gaira babu dalili, shine jahilci, wato rashin ilmin addini da na boko da su Fulani da mutanan karkara ke fama da shi. Da yawa masu barna a cikinsu, ba su san Allah ba, balle su san daidai, ko akasin haka. Babu karatun addini, babu na boko, babu ilimin zamantakewa, babu tunanin mutuwa da sakamako.

A wani rahoto da gidan jaridar BBC Hausa ya tattara kuma wallafa a kafafen sadarwar zamani, an nuna wani kasurgumin dan fashin daji yana cewa shi baya jin komi a ransa don ya kashe mutum ko ya kona gari.

Labarai Masu Nasaba

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

Babban Malamin addini musulunci da ke Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, wanda ya shiga cikin dazuka ya kuma gana da wadannan ‘yan fashi ya hakikance cewa manyan dalilan ricikin sun fi ta’allaka da rashin ilimin bambance fari da baki, masu tayar da zaune tsaye da ke rayuwa a cikin daji, ba su san inda kansu yake musu ciwo ba, babu Sallah, babu salati, saboda haka ya zama wajibi a tashi tsaye wajen ganin an koyar da su, manyansu da yaransu ilimin addini da na boko, domin su san Allah da kuma azabar da ke tattare da mutumin da yake aikata miyagun laifuka, su kuma san hakkin da ya rataya a kansu a matsayinsu na ‘yan kasa.

Ganin haka ne ya sa Gidauniyar Malam Inuwa (Malam Inuwa Foundation) da ke garin Hadejia a Jihar Jigawa, ta tashi haikan domin tsamo da irin wannan mutanen da ke fama da duhun jahilci, inda ta himmatu wajen koyar da su ilimin addini da na zamani, ba don komai ba sai don su san kansu, da kuma hakkokin da suka rataya a wuyansu a matsayinsu na ‘yan adam, kuma Musulmi.

Gidauniyar Malam Inuwa, wadda aka kafa da manufar tallafawa marayu, masu karamin karfi, koyawa matasa sana’o’i domin dogaro da kai, ilimantar da al’umma tare da wayar musu da kai, ta himmatu wajen ganin al’ummar karkara da suke fama da karancin ilmin addini, sun samu malamai da makarantu domin a koyar da su ilmummuka na kowane fanni.

A irin kokarinta na ba da gudunmawa wajen magance matsalar tsaro da ta addabi al’ummar Arewa Maso Yammacin Nijeriya, tare da fatan da take da shi na kyautata rayuwar al’umma, Gidauniyar ta Malam Inuwa, ta dauki nauyin koyar da yaran Fulani hadi da iyayensu da ke rayuwa a cikin dazuka ilimin Alkur’ani mai girma har na tsawon shekara guda a Rugar Gadan Maje dake karamar hukumar Taura a Jihar Jigawa.

Shirin Gidauniyar, wadda ke samun tallafi na musamman daga Shugaban Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwar Zamani ta Kasa, Malam Kashifu Inuwa, ya faro ne da garin Rugar Gadan Maje da ke cikin yankin karamar hukumar Taura a Jihar Jigawa, a matsayin gwaji, inda aka shafe tsawon shekara guda ana koyar da manya da yara ilimin sanin duniya da lahira.

Gidauniyar Malam Inuwa
Makarantar magidanta da gidauniyar ta xauki nauyi a Jigawa

Yayin yaye wasu daga cikin daliban da suka kammala karatu a makon da ya gabata, Malam Kashifu Inuwa, wanda ya samu wakilcin Dakta Husaini Yusuf Baba, ya yi jinjina ga Malaman da suke koyarwar, inda ya bayyana muhimmancin karantar da al’umma sakon da Allah Ta’ala ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) na hakikanin addinin Musulunci, sanin ya kamata da kuma wanzar da adalci a tsakanin al’umma.

Har ila yau, a yayin kaddamarwar, Sarkin Taura, Alhaji Rabi’u, gami da Wakilin Hakimin Taura, Dagacin ‘Yan Yanga, Alhaji Auwalu Usman, sun yi jinjina tare da godiya da addu’ar fatan alheri ga mai girma jagoran gidauniyar, Malam Kashifu Inuwa kan kokarinsa na ilimantar da jama’arsu, a cewarsu, ilimi ne kadai zai iya saita al’umma su hau kan hanya madaidaiciya.

A tattaunawar da aka yi da wasu mazauna garin Taura sun tabbatar da cewa kafin fara wannan karatu, Fulanin wannan ruga suna yawan aikata ayyukan ta’addanci kamar sata, fashi, da raunata mutane babu gaira babu dalili, amma daga lokacin da Gidauniyar Malam Inuwa ta fara koyar da su karatu, aka samu zaman lafiya a yankin.

Fulanin wannan ruga sun nuna farin cikinsu matuka, sun kuma gamsu da cewa yanzu an san da zamansu, don ba su taba samun manyan baki da suka halarci rugarsu ba sai ta dalilin wannan shiri.

Domin wanke musu zuciya ta hanya koyar da su da ilmi, shugaban Gidauniyar ta Malam Inuwa ya yiwa Fulanin alkawarin kammala Masallacin da aka fara ginawa cikin gaggawa, tare da samar da abubuwan da kowane Masallaci yake da bukata don a gudanar da ibada, sannan za a samar musu makarantu na musamman don koyar da su ilmi.

Hakika wannan ci gaba ne mai girma wanda zai taimaka wa al’umma matuka wajen sanin Allah da kuma dakile matsalar gurbacewar tunani da ake samu a tsakanin mutanen da ke rayuwa a cikin daji da rugage, Gidauniyar Malam Inuwa ta himmatu wajen aikin hadin gwiwa da sauran gidauniyoyin samar da ci gaba domin magance matsalolin al’umma dabandaban ta hanyar aiwatar da tsaretsaren gano matsalolin jama’a da bullo da dabarun magance su, musamman samar da walwala a tsakanin al’umma.

Gidauniya ce ta mutane masu son taimakon al’umma duba da karuwar yara marayu sanadiyyar tashe-tashen hankula da fadace-fadace da ake fama da su a yankin arewa, shi ya sa ta fito da tsaruka domin gudanar da ayyukan taimako, agaji, da jin-kai daidai da bukatar al’umma.

Gidauniyar Malam Inuwa ta himmatu kwarai wajen taimakon al’umma, domin a kwanakin baya ma ta yi hadin gwiwa da Kungiyar Matasa Musulmai ta Duniya, ‘World Assembly of Muslim Youth’ (WAMY), da Gwamnatin Jihar Jigawa, inda ta yi wa akalla mutane dubu takwas da dari bakwai da talatin (8730) aikin ido tare da raba musu gilashi kyauta, wanda ya gudana a babban asibitin Hadejia.

Haka zalika, Gidauniyar da tallafin gidauniyar katar ta kara shirya wani aikin gyaran idon da ba da magani da gilashi kyauta wanda jimillar mutane dubu biyu da dari da bakwai (2107) suka ci gajiyarsa a babban Asibiti da yake karamar hukumar Gumel.

Ba ta tsaya a nan ba, Gidauniyar, har ila yau, da hadin gwiwar takwararta ta katar, ta gabatar da shirin tallafa wa matasa maza da mata, ta hanyar koya musu sana’o’i daban-daban, tare da ba su tallafin dogaro da kai, domin sanya farin ciki a zukatansu da hana fadawa yanayin da ka iya jefa al’umma cikin tashin hankali da rashin zaman lafiya.

Gidauniyar Malam Inuwa na ci gaba da samun yabo, jinjina, da addu’ar fatan alkhairi daga al’umma bisa namijin kokarin da take yi na tallafa wa marasa karfi a fannoni da dama.

 

Mubarak ya rubuto daga Abuja


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AddiniGidauniyar Malam InuwaIlimiJigawaKarkaraRugageTallafiYaboYaki Da Jahilci
ShareTweetSendShare
Previous Post

Me Ya Sa Ba A Fara Shekarar Hijirah Da Ranar Badar Ko Ranar Cikar Wahayi Ba? (I)

Next Post

GORON JUMA’A

Related

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 
Bakon Marubuci

Dabi’a: Yadda Ake Gini Da Rusa Ta 

18 hours ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)

2 weeks ago
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)
Bakon Marubuci

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (2)

3 weeks ago
Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
Bakon Marubuci

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

2 months ago
Waraka Daga Bashin Ketare
Bakon Marubuci

Waraka Daga Bashin Ketare

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]

3 months ago
Next Post
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

LABARAI MASU NASABA

Matatar Dangote Zata Fara Rarraba Man Fetur Da Dizal A Nijeriya

Matatar Dangote Zata Fara Rarraba Man Fetur Da Dizal A Nijeriya

June 15, 2025
Wata Sabuwa: Malaman Jami’ar Tarayya A Kano Sun ƙi Amince Wa Da Zaɓen Sabon VC

Wata Sabuwa: Malaman Jami’ar Tarayya A Kano Sun ƙi Amince Wa Da Zaɓen Sabon VC

June 15, 2025
PLA Reshen Kudancin Kasar Ta Yi Sintiri Na Hadin Gwiwa A Tekun Kudancin Sin

PLA Reshen Kudancin Kasar Ta Yi Sintiri Na Hadin Gwiwa A Tekun Kudancin Sin

June 15, 2025
An Bude Bikin Fina-Finai Na Kasa Da Kasa Karo Na 27 Na Shanghai

An Bude Bikin Fina-Finai Na Kasa Da Kasa Karo Na 27 Na Shanghai

June 15, 2025
Yansanda Sun Fara Tsananta Daukar Mataki Kan Yan Daba A Kano

Yansanda Sun Fara Tsananta Daukar Mataki Kan Yan Daba A Kano

June 15, 2025
Dan Asalin Tudun Loess

Dan Asalin Tudun Loess

June 15, 2025
Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

June 15, 2025
Ganduje Ya Noƙe Kan Furta Ko Shettima Zai Yi Takara Da Tinubu A 2027

Ganduje Ya Noƙe Kan Furta Ko Shettima Zai Yi Takara Da Tinubu A 2027

June 15, 2025
Wang Yi Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Isra’ila

Wang Yi Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Isra’ila

June 15, 2025
APCn Kaduna Ta Mara Wa Tinubu, Uba Sani Da Kakakin Majalisa Abbas Baya Don Wa’adi Na Biyu

APCn Kaduna Ta Mara Wa Tinubu, Uba Sani Da Kakakin Majalisa Abbas Baya Don Wa’adi Na Biyu

June 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.