Gwamnan Jihar Kataina, Aminu Bello Masari ya bayyana bukatar ganin masu iko na taimaka wa masu karamin karfi a cikin jihar.
Gwamna Masari ya fadi hakan ne a lokacin da yake kaddamarwa da kuma raba kayayyakin aikin asibitin kashi da litattafan karatu da kekunan tura marasa lafiya da sauran kayan kula da lafiyar yara da gidauniyarsa suna Aminu Masari Foundation hadin gwiwa da kungiyar Bruderlife suka shirya kuma ya gudana a dakin taron shugaban kasa da ke gidan gwamnatin Jihar Katsina.
- Yajin Aikin ASUU Na Barazana Ga Ci Gaban Kasa
- Bai Kamata A Maida Iraki Fagen Takarar Siyasa Tsakanin Bangarori Daban-daban Ba -In Ji Kasar Sin
Ya ce gidauniyar da aka assasa kimanin shekaru 18 da suka gabata, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimaka wa mabukata musamman ma a kan abubuwan da suka shafi ilimi da makamantansu.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar Kabir Mashi wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Abdullahi Imam ya yi kira ga mutanen da ke niyyar ba da gudummuwarsu zuwa ga mabukata da su ba da ta hanyar gidauniyar.
Tun da farko a jawabinsa sakataren gidauniyar, Ibrahim Ahmed Katsina, ya ce gidauniyar na gudanar da ayyukan taimakon al’umma daban-daban da suka shafi aikin idon a fadin Jihar Katsina.