Gidauniyar TY Buratai Humanity Care Foundation ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ƙara albashin ma’aikata a 2025 don taimakawa su iya biyan buƙatun rayuwar yau da kullum. Tsohon COAS Laftanar Janar TY Buratai ya bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Ma’aikata, inda ya nuna cewa ma’aikatan tarayya da na jihohi ba su iya biyan buƙatun iyalansu.
A wata sanarwa, shugaban gidauniyar Ibrahim Danfulani ya jaddada cewa bikin Ranar Ma’aikata ya kamata ya zama tunatarwa ga yaƙin neman ingantaccen yanayi na aiki da adalci. Ya kuma yaba wa ma’aikatan Nijeriya saboda gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban ƙasa.
- Buratai Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’Adua
- Buratai Ya Ɗauki Ɗamarar Ɗaga Likkafar Fasaha a Nijeriya
Janar Buratai ya ƙara da cewa: “A ruhin shirin ‘Renewed Hope Agenda’, ƙaruwar albashi zai sake sanya ma’aikata murna.” Ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu kan sauye-sauyen da ta yi don inganta yanayin aiki, yana mai cewa ma’aikata su dage da aikin gina ƙasa.
Gidauniyar ta kuma tabbatar da ci gaba da tallafawa marasa galihu ta hanyar shirye-shiryen agaji. Ta yi kira ga haɗin kai tsakanin dukkan ɓangarori don tabbatar da an biya ma’aikata albashi mai kyau.
A ƙarshe, gidauniyar ta nuna goyon bayanta ga ma’aikatan Nijeriya, tare da kira ga gwamnati da ta saurari buƙatunsu domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp