Gamayyar kungiyar ‘ya’yan Sarakunan Arewacin Nijeriya a karkashin gidauniyar “In Kaji Tambura”, sun bayyana goyon bayansu a nadin Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III a matsayin shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta kasa (NCTRN) na dindindin.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an yi ta cece-kuce dangane da batun nadin Sarkin Musulmi da Ooni na Ife a matsayin shugabanni na dindindin a majalisar sarakunan gargajiya ta kasa.
- Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
A wata sanarwa da ta fitar a Gombe ranar Laraba, Sakataren kungiyar, Yarima Mahmood Aminu Adamu, ya yi watsi da adawa da nadin da kungiyar Middle Belt Forum (MBF) ta yi a matsayin “abinda bai dace ba duba da yanayin hadin kan kasa”.
Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.
Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.
Sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya yi namijin kokari wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da hadin kan kasa.
Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa, da fadar shugaban kasa, da sauran al’ummar Nijeriya da su goyi bayan nadin, inda ta ce hakan zai karfafa cibiyoyin gargajiya da kuma samar da hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp