A cikin wata kwakkwarar sanarwa da gidauniyar TY Buratai Humanity Care Foundation ta fitar, ta yi kira da a hukunta ‘yan kasashen masu manyan shagunan sayar da kayan alfarmada ke Abuja a Nijeriya, wadanda ke hana ‘yan Nijeriya shiga siyayya.
Gidauniyar karkashin jagorancin shugabanta Amb Ibrahim Dahiru Danfulani Sadaukin Garkuwan Keffi da Betara na Biu, sun nuna matukar damuwarsu kan yadda babban kanti ya ke nuna wariya, wanda ke bai wa ‘yan kasar China damar shiga da sayen kayayyaki, tare da hana ‘yan Nijeriya yin hakan.
- Sauya Sheka: Jam’iyyu Na Shirin Tilasta Kafa Dokoki Masu Zafi A Kan ‘Yan Majalisa
- Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida: AMDF Ta Nemi A Bai Wa ‘Yan Jarida Kariya A Afirka
Babban Majibincin gidauniyar, Mai Girma Ambasada Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai (Rtd) CFR, tsohon babban hafsan soji, ya yi Allah-wadai da yadda masu manyan kantunan ke nuna wariya, inda ya kwatanta hakan da wariyar launin fata.
Ya kuma jaddada cewa babu wani dan kasar waje da ya kamata a tauye masa hakkinsa a Nijeriya matukar ya bi dokokin kasar.
Janar Buratai ya nuna shakku kan wariyar da ‘yan kasashen waje ke yi wa ‘yan kasa da tsara masu yadda za su yi rayuwa a kasarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp