Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya tsakanin Sin da Afrika, tare da gabatar da shawarar gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya a sabon zamani, domin cimma tsaro na bai daya. Shugaban ya bayyana haka ne yayin taro karo na biyu na ministocin kasashen Sin da Afrika kan dangantakar tsaro da zaman lafiya.
Amini na kwarai shi ke kasancewa da amininsa a ko wanne hali. Matsalar tsaro batu ne da ke ciwa kasashen Afrika tuwo a kwarya, la’akari da mummunan tasirinta ga zaman lafiya da ci gaba. Babu wata kasa da za ta samu ci gaban da take muradi, muddun ta na fama da matsalar tsaro. Don haka a matsayinta na Aminiya ga kasashen Afrika, kuma babbar kasar da ta san ya kamata, Sin na kokarin hada gwiwa da su domin magance matsalar.
Kasar Sin ce kasa mafi yawan jama’a a duniya, amma kuma, tana cikin kasashe kalilan dake more zaman lafiya da tsaro a duniya. Yadda kasar Sin ta ke kokarin karfafa hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya da kasashen Afrika, ya nuna cewa ta damu da yanayin da suke ciki, kuma tana muradin taimaka musu.
Har ila yau, kasashen Afrika da Sin na da kamanceceniya ta fuskar yawan al’umma, kuma kasashe masu tasowa, wannan ya samar wa kasashen Afrika wata dama mai sauki na koyi tare da aiwatar da dabarun Sin ba tare da samun matsala ba.
Taimakon kasar Sin daya ne daga cikin kyawawan manufofinta da suka saba da na kasashen yamma, wadanda suke ingiza rikici da yin katsalandan cikin harkokin gidan kasashe, har ma da rura wutar rikici da uwa uba kitsa juyin mulki.
Ko da yake, wanda ya gaza tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kare al’ummarsa, ina zai samu gogewar bayar da shawara ko kuma zama abun koyi?
Duk wanda yake bibiyar kasar Sin, ko yake zaune a kasar, dole ne ya jinjinawa irin kwanciyar hankalin dake akwai.
Alkaluman kididdiga sun shaida cewa, yadda al’umma suke jin dadin yanayin tsaro a kasar Sin, ya karu zuwa kaso 98.62 a shekarar 2021, daga kaso 87.55 da ya kasance a shekarar 2012.
A ganina, hadin gwiwa a fannin tsaro da kasar Sin, abu ne da ya kamata gwamnatocin Afrika su dauka da muhimmanci idan suna son shawo kan matsalolin da ke addabarsu.
Shawarar gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ba makawa kyakkyawar dabara ce da zata yi gagarumin tasiri a Afrika.
Wannan na nufin samun tsaro kamar kasar Sin har ma da ci gaba da kwanciyar hankali da wadata tamkar kasar Sin.