Wani bincike na MSN Money da ke kula da hada-hadar kudi da hannayen jari da kadarori da lamuni a duniya ya bayyana gine-gine mafi tsada a duniya.
Binciken ya fito da gini 30 mafi tsada a duniya, kuma Saudiyya ce kan gaba inda take da gini biyu a Makkah mafi darajar kudi a duniya.
- Bayan Biyan Kudin Fansa, Kasurgumin Dan Bindiga Ya Saki Daliba 4 Na Kwalejin Yauri
- Bukatar Magidanta Su Sa Ido Kan Yadda ‘Ya’yansu Za Su Yi Bikin Sallah
Binciken MSN Money da aka gudanar a 2019 ya nuna cewa, Masallacin Ka’abah na Makkah, wato Masjid al-Haram shi ne gini mafi tsada a fadin duniya kuma da tazara sosai.
Fadada ayyukan masallacin a tsawon shekaru ya kara wa ginin masallacin daraja fiye da duk wani gini a duniya, inda MSN Money ya ce darajarsa ta kai Dala biliyan 100.
Ginin Abraj Al-Bait a Makkah mai kunshe da otel da dakuna na kasaita da kantuna shi ne na biyu mafi tsada a duniya inda darajarsa ta kai Dala biliyan 16.
Babban wurin shakatawa a Singapore da ake kira Maina Bay Sands resorts ne na uku da darajarsa ta kai sama da da Dala biliyan shida.
Ginin Burj Khalifa, na Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa ne na 30 a jerin gine-gine mafi tsada a duniya, duk da cewa shi ne gini mafi tsawo a duniya.
Masallacin Ka’aba, Makkah: Dala Biliyan 100
Wuri mafi tsarki a addinin Islama kuma masallaci mafi girma a duniya Masallacin Ka’abah a Makkah kasar Saudiyya wanda ke daukar mutum sama da miliyan hudu lokacin aikin Hajji an kiyasta cewa darajarsa ta kai Dala biliyan 100.
Tazarar darajar kudin ginin na Masallacin Ka’aba ana ganin da wuya a samu wani ginin da zai kere shi, duk da abubuwa na sauyawa a duniya da kuma farashin kayayyaki musamman kadarori na gine-gine.
Ginin Abraj Al Bait, Makkah: Dala biliyan 16
Dogon ginin Makkah Abraj Al Bait da ke kusa da Masallacin Ka’aba wanda aka gina a 2012 an bayyana cewa darajarsa ta kai Dala biliyan 16.
Abraj Al Bait an gina shi kan Dala biliyan 15 domin saukar da mahajjata musamman shugabanni da masu hannu da shuni. Baya ga girmansa, ginin shi ke da fuskar agogo mafi girma a duniya.
Ginin Abraj Al Bait shi ne na biyu mafi darajar kudi a duniya bayan Masallacin Ka’aba a Makkah.
Wurin shakatawa Marina Bay Sands, Singapore: Dala biliyan 6.2
Babban wurin shakatawa Marina Bay Sands na Singapore mai kunshe da otel da dakunan kasaita shi ne na uku mafi tsada a duniya wanda darajarsa ta kai Dala biliyan 6.2.
Marina Bay Sands wanda aka kammala a 2010 an gina shi ne kan kudi biliyan 5.5, kuma yanzu darajarsa ta karu.
Shelkwatar Kamfanin Apple, Cupertino: Dala Biliyan Biyar
Ginin Apple Park, hedikwatar kamfanin Apple da ke Cupertino a California kasar Amurka shi ne na hudu mafi tsada a duniya.
Apple, kamfanin mafi tsada a duniya an bayyana yana da rarar kudi fiye da dukiyar da kasashe masu tasowa suka mallaka.
Coci-Coci Da Aka Mayar Masallatai Da Masallatan Da Suka Koma Coci-Coci
Ba abin mamaki ba ne idan kamfanin ya kashe Dala biliyan biyar domin gina katafariyar hedikwatarsa.
Ginin Cosmopolitan, Las Begas: Dala biliyan 4.4
Ginin otel din Cosmopolitan mai yawan daki 3,027 ya lakume Dala biliyan 3.9 wajen gina shi a 2009.
Ginin otel din da ke da babban wurin caca da kuma dakin taro mai yawan kujera 3,200 shi ne gini na biyar mafi tsada a duniya.
Sabon ginin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya, New York: Dala biliyan 4.1
Sabon dogon ginin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya da ke New York mai tsawon kafa 1,776 shi ne na shida mafi tsada a duniya, a cewar MSN Money.
Ginin da ake kira One World Trade Center an kammala shi ne a 2012 kan kudi Dala biliyan 3.8 (£2.7bn), amma darajarsa yanzu ta haura Dala biliyan hudu.
Ginin shi ne mafi girma yanzu a Amurka.
Ginin Majalisar Bucharest: Dala Biliyan 3.9
Ginin na otel mai kama da fadar sarki a Dubai yana dauke da masauki 397 da manyan wuraren shakatawa da kantina da wuraren cin abinci na kasaita.
Darajar ginin da aka kammala a 2005 an bayyana ta kai Dala biliyan 3, yanzu kuma darajarsa ta haura haka.
Wurin shakatawa na Wynn Resort, Las Begas: Dala biliyan 3.4
Yana daya daga cikin kyawawan otel na duniya da ke rukunin manyan gidajen caca na casino a Las Begas.
A 2005 aka kaddamar da wurin shakatawar na Wynn. Kudin aikin ginin wannan katafaren gininmai yawan daki 2,716 ya kai Dala biliyan 2.7, yanzu darajarsa ta kai fiye da Dala biliyan 3.4.
Fadar Sarkin Brunei Istana Nurul Iman: Dala biliyan 3.3
An gina ta a 1984 kan kudi Dala biliyan 1.4, Fadar Sarkin Brunei ita ce fada mafi girma a duniya kuma har yanzu ginin na nan a matsayin gidan sarauta.
Ginin ne fadar gwamnatin Brunei da ke da yawan dakuna 1,788 da kuma katafaren dakin taro da ke daukar mutane 5,000.
Sultan na Brunei, Hassanal Bolkiah na cikin manyan attajiran duniya.