Adadin wadanda suka mutu biyo bayan girgizar kasar da aka samu a Turkiyya a ranar Litinin ya karu zuwa 19,388 kamar yadda shugaban kasar Turkiyya, Erdogan ya bayyana.
Adadin kuma a makwabciyar kasar Syria ya kai 3,377 wanda hakan ke nufin adadin a kasashen biyu ya haura 23,000.
- Babu Wani Dan Nijeriya Mai Hankali Da Zai Zabi APC Da PDP – Kwankwaso
- APC Ta Dage Yakin Zaben Shugaban Kasarta A Kano
Erdogan ya ce sama da mutum 77,700 sun jikkata a Turkiyya, inda ya kara da cewa za a sassautawa wadanda suka jikkata haraji.
Tun da fari, ya amsa cewa gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba cikin gaggawa kan wannan balahira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp