Shugaban majalisar gudanarwar kasar Myanmar, babban janar Min Aung Hlaing, ya mika godiyarsa a yau Lahadi ga mambobin kungiyar likitoci masu aikin ceto ta Yunnan ta kasar Sin bisa taimakon da suka bayar a kan lokaci, bayan wata girgizar kasa mai karfi ta afku a kasar ta Myanmar a ranar Jumma’ar da ta gabata.
Shugaban na Myanmar ya ziyarci asibitin Ottara Thiri mai zaman kansa da ke Nay Pyi Taw, babban birnin kasar Myanmar a yau Lahadin, inda ya gode wa tawagar masu aikin ceton ta kasar Sin, wacce ta garzaya yankin da abin ya shafa a farkon lokaci domin kai dauki.
- Sin Da Jamhuriyar Congo Za Su Karfafa Raya Hadin Gwiwar Sin Da Afrika
- Masana’antar Shirya Fina-Finan Kagaggun Labaran Kimiyya Da Fasaha Ta Sin Ta Samu Yuan Biliyan 108.96 A 2024
Tawagar masu aikin ceton ta kasar Sin da ta fito daga lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar, tare da hadin gwiwar ma’aikatan ceto na Myanmar, sun ceto wani dattijo da ya makale a girgizar kasar da ta afku a Nay Pyi Taw da misalin karfe 05:00 na asubahin yau Lahadi.
Mutumin dai ya shafe kusan sa’o’i 40 a makale a karkashin baraguzan ginin asibitin da ke birnin. Bayan aikin ceton gaggawa da aka yi cikin dare, mutumin shi ne na farko da tawagar kasar Sin ta ceto shi da rai, bayan da ta isa yankin da girgizar kasar ta shafa a Myanmar, ranar Asabar.
Tawagar ta Sin mai mambobi 37 ta garzaya yankin dauke da rantsattsun na’urorin gano mutane masu rai, da na’urorin da ke yin gargadi a kan girgizar kasa a kan kari, da wayoyin tauraron dan’adam, da na’urorin aiki masu tashi sama, da sauran na’urorin ceto domin gudanar da ayyukansu na ceto.
Akwai karin tawagogin ceto da dama na kasar Sin da suka shiga ayyukan ba da agaji tare da takwarorinsu na Myanmar.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.7 ta afku a kasar ce da ke kudu maso gabashin Asiya, a ranar Jumma’ar da ta gabata. A jiya Asabar da dare, tawagar yada labarai ta majalisar gudanarwar kasar ta bayyana cewa, sama da mutum 1,700 ne suka mutu, kana sama da 3,400 suka jikkata, yayin da kuma kimanin 300 suka bace, a kakkarfar girgizar kasar da ta faru a kasar ta Myanmar.
A yinin yau Lahadi kuma, wani jirgin saman kamfanin China Eastern Airlines ya tashi daga Kunming, babban birnin lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, dauke da kayayyakin agaji kimanin tan 7.3 zuwa kasar Myanmar da girgizar kasa ta afka wa.
An nemo kayayyakin agajin ne tare da tattara su a birnin na Yunnan, wadanda suka hada da tufafi, da magunguna, da taliya, da tantuna da sauran kayayyakin masarufi da ake bukata yau da kullum. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp