Da safiyar yau Alhamis ne wutar gobara ta tashi a wani sashin cocin Dodds Methodist Church Cathedral tare da lalata kadarorin da suka zarce na miliyan 10 a Uzuakoli da ke kusa da Umuahia a jihar Abia.
Da ya ke ganawa da LEADERSHIP a inda lamarin ya faru, Jakadan cocin, Rabaran Anyanwu James Alozie, ya nuna godiyarsu ga Allah bisa yadda ya taimakesu tare da kawo dauki cikin lamarin da har ba a samu mutuwa ba.
Ya roki masu hannu da shi da su taimaka wajen maido da abubuwan da aka yi asararsu.
Malamin ya kuma gode wa jama’a a bisa yadda suka fito suka tayasu kashe gobarar lokacin da take ci.
Shi kuma a bangarensa, Rt Rev Chibuikem Johnson ya ce wutar ta lalata kadarorin da suka hada da kwamfutoci, injuna da wasu muhimman takardu hadi da wasu abubuwan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp