Wata gobara da ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Munna Albadawi, a Ƙaramar Hukumar Jere a Jihar Borno, ta yi ɓarna mai yawa tare da kashe wani yaro ɗan shekara bakwai.
Shugaban sansanin, Malam Babangida Mahmud, ya ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 3 na Asuba a ranar Alhamis, inda ta laƙume tantuna da ɗakunan kwanan ‘yan gudun hijira da kuma kayayyakinsu.
- Nijeriya Da Brazil Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Kasuwanci Ta Dala Biliyan 1
 - Gaggan Masu Garkuwa Da Mutane 10 Da Kayan Aikinsu Sun Shiga Hannu A Kano
 
Har yanzu ba a tantance adadin ɓarnar da aka yi ba.
Jami’an hukumar kashe gobara da haɗin gwiwar hukumomin tsaro sun yi ƙoƙari wajen shawo kan wutar bayan ta yi mummunan ta’adi.
Yaron da ya rasu a gobarar mai suna Abubakar Gargar, an gano gawarsa kuma an miƙa wa iyalansa don jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.
A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar.
			




							








