Gobara ta kone hedikwatar ‘yansandan Jihar Kano da ke Bompai da yammacin ranar Asabar.
An tattaro cewa gobarar ta tashi ne wani ofishi ta kuma bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin kakakin rundunar, ofishin mataimakin kwamishinan ‘yansandan da sauransu.
- Gwamnatin Zamfara Ta Gano Likitocin Bogi 199 A Jihar
- Wasu Jiga-jigan APC Da Ba A Jin Duriyarsu A Yakin Neman Zaben Tinubu
An tattaro cewa dukkan ofisoshin da ke saman benen ginin na shekarar 1967 gobara ta kone su, sai ofishin kwamishinan ne kadai ya rage.
“Mun yi kokarin kashe gobarar da ta tashi a wani ofishi ta hanyar amfani da na’urar kashe gobara ta hannu amma sai wutar ta bazu zuwa wasu ofisoshi da yawa.
‘Yan kwana-kwana sun isa wurin ne kusan sa’o’i biyu bayan tashin gobarar,” wata majiya ta shaida wa manema labarai.