Gwamna Bello Matawalle, ya ce gwamnatin Jihar Zamfara ta gano akalla likitocin bogi 199 da ke cikin tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnatin jihar.
Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Maradun, hedikwatar karamar hukumar Maradun ta jihar.
- Mutum Daya Ya Mutu A Rikicin Fulani Da Patigi A Kwara
- Zargin Sace 89trn: Dan Takara A Kano Zai Maka Buhari A Kotu
A cewar gwamnan, duk da cewa gwamnatin jihar na biyan albashi ga likitoci 280 duk wata, amma ta gano likitoci 81 ne kawai ke aiki a fadin jihar.
Ya kuma bayyana cewa tuni ya gana da kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar kan yadda za a gano wadancan likitocin bogi 199 da suka dauki tsawon lokaci suna karbar albashi ba bisa ka’ida ba.
Matawalle ya bayyana cewa, gano likitocin bogin ya biyo bayan ci gaba da binciken bayanan da ake yi wa daukacin ma’aikatan jihar ta ofishin shugaban ma’aikatan jihar.
An ce aikin tattara bayanan na nuni ne da shirin gwamnatin jihar na fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga ma’aikatan jihar.
“Matsalar ita ce, da zarar mun ce za mu aiwatar da shi (N30,000), ba za mu iya cewa za mu biya mutane kai tsaye haka ba. A’a, akwai tsari,” in ji Matawalle.
“Mun samar da tsari, kuma abin takaici, a lokacin aiki, an gano cewa akwai likitoci sama da 280 da suke karbar albashi daga gwamnatin jihar nan, amma a gaskiya muna da likitoci 81 ne kawai na gaskiya a Jihar Zamfara.
“Kungiyar kwadago ta tabbatar min dalilin da ya sa suka jinkirta shirin – cewa suna son tabbatar da cewa abubuwa sun tafi daidai saboda ba za mu iya ci gaba da hakan a matsayin gwamnati ba.”
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa babu wani ma’aikaci na gaskiya da gwamnatinsa za ta yi murabus dangane da aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000.
“Ba zan sake mayar da kowa ba. A gaskiya zan ba su gidajen (ma’aikatan gwamnati) na duk ma’aikatan gwamnati. Na gina musu gidaje 450 wadanda babu wanda ya san su, amma ranar Lahadi zan ba su makullin,” in ji shi.