Gobara ta lakume shagunan sayar da hatsi 19 dauke da buhunan hatsin dubu 19 a kasuwar Gombi da ke Karamar Hukumar Gombi a Jihar Adamawa.
Umar Nyalli, sakataren kungiyar ‘yan kasuwar hatsin, ya bayyana haka lokacin da mataimakiyar gwamnan jihar ta kai ziyarar jaje ga ‘yan kasuwar.
- Zargin Sata: ‘Yar Majalisa Ta Yi Murabus A New Zealand
- Ina Rubutu Ne Da Ra’ayin Kawo Gyara Ga Rayuwar Al’umma – Aisha Sani
Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon jefar da taba-sigari a shara kusa da shagunan.
A cewar Nyalli, ‘yan kasuwar sun yi asarar komai na shagunan 19, ya ce komai ya lalace, saboda ba a iya cire komai daga cikin kayayyakin ba.
“Mun yi asarar buhunan masara, gyada, wake da kuma ‘ya’yan tumatir, muna kira ga gwamnati da ta kawo mana dauki” in ji Nyalli.
Da ta ke jawabin jajanta wa ‘yan kasuwar mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta jajanta wa ‘yan kasuwar, ta ce bala’i ne babba da ya shafe su.
Mataimakiyar gwamnan ta shawarci ‘yan kasuwar da rungumi kaddara.
“Ku dauka wannan jarabawa ce daga Allah, ku yi imani Allah shi zai mayar muku da abin da kuka rasa” in ji Farauta.
Haka kuma mataimakiyar gwamnan, ta roki hukumomin da abin ya shafa da su fadakar da ’yan kasuwar hanyoyin da za su bi, wajen kaucewa aukuwar gobara a nan gaba a yankin.
Da yake jawabi, hakimin Gombi, Alhaji Usman Sarki Fada, ya gode wa gwamnatin jihar bisa jajantabwa mutanen da gobarar ta shafa.