Sabuwar ‘yar majalisar New Zealand ta yi murabus saboda zarge-zargen cewa ta yi dauke-dauke, zargin da ‘yansanda ke bincike a kai.
An yi zargin cewa Golriz Ghahraman, ‘yar jam’iyyar Green Party, ta yi sata har sau uku a wasu shagunan sayar da kayan sawa da dangoginsu biyu- daya a Auckland, dayan kuma a Wellington.
- Mahalartan WEF: Sin Muhimmiyar Injin Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa
- Gazawar Gwamnati Ta Tsananta Fatara Da Rashin Tsaro A Nijeriya –Atiku
Tsohuwar lauya a hukumar kare hakkin dan‘Adam din ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa tarihi ne a 2017 a matsayin ‘yar gudun hijira ta farko da ta shiga gwamnatin.
Ta taba rike mukamin sashen shari’a na jam’iyyarta.
Sai dai ta ce galabaitar da aikinta ke jefa ta ne ya sa ta aikata abin da ba halinta ba ne.
“Na bai wa mutane da dama kunya don haka ina mai basu hakuri,” In ji ta.
Mis Ghahraman ta tsere ne daga kasar Iran lokacin tana yarinya tare da iyalinta, wadanda aka ba mafakar siyasa a kasar New Zealand.
Murabus dinta a ranar Talata ya zo ne bayan wasu hotunan CCTB sun nuna lokacin da ake zargin ta dauki wata jakar mata ta kawa a shagon sayar da kayayyaki na Auckland.
Ba a taba samun ‘yar majalisar mai shekara 42 da aikata wani laifi ba.
Yayin da yake mayar da martani kan murabus dinta, daya daga cikin shugabannin jam’iyyarta, James Shaw ya ce Mis Ghahraman ta fuskanci “munanar barazana da suka shafi cin zarafi, duka da kuma kisa tun lokacin da aka zabe ta a matsayin ‘yar majalisa”.