Gobara ta tashi a wani sashen babbar kasuwar Onitsha, da ke a jihar Anambra, sai dai, ba a tabbatar da abinda ya haddasa ta ba.
Iftila’in wanda ya auku a tsakar daren jiya lahadi, wani dan kasuwa a kasuwar mai suna Obenta Jude ya ce, wasu shaguna biyu sun kone a wani sashe na kasuwar da akafi sani da titin Kano.
Jude ya kara da cewa, jami’an kashe gobara sun zo kasuwar, inda suka kashe gobarar.
Shugabar hukumar kashe gobara na jihar Injiniya Martin Agbili ya tabbatar da aukuwar ifitila’in, inda ya ce, hukumar ta yi gaggawar tura Jami’anta zuwa kasuwar don kashe gobarar.
A cewar Shugabar hukumar, da kimanin karfe 2.20 na daren jiya ne hukumar ta samu labarin tashin gobarar bayan kiran wayar a kawo dauki, inda ya kara da cewa, hukumar ta tura jami’anta don su kashe gobarar.