Wata wutar gobara mai ban mamaki ta tashi da sanyin safiyar Talata, a babbar kasuwar Onitsha, a jihar Anambra.
Babbar Kasuwar ana cewa, ita ce kasuwa mafi girma a yammacin Afirka, kuma tana da dimbin ‘yan kasuwa, wadanda galibi masu shigo da kayayyaki ne, kuma suna hada-hadar kayayyaki iri daban-daban.
Wata majiya daga Mista Barth Ifediora, wanda ya bayyana fargabar wutar, ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Talata, a wani sashe na kasuwar da aka fi sani da fadar White House.
Fadar White House ita ce ofishin shugabannin kasuwar, wani gini ne mai hawa biyu wanda yake da ofisoshi da dama, da dakunan taro a hawa na daya da na biyu, sai kuma shaguna a kasa.
Wata majiya ta ce: “Yankin da gobarar ta fi shafa shi ne bangaren shagunan da ke karkashin WhiteHouse, inda ake sayar da kayan yadi masu tsada.”