Hukumomi a Jihar Borno sun tabbatar da cewa gobara ta tashi a rumbun ajiye makamai na barikin sojoji da ake kira Giwa Barracks da ke Maiduguri.
Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar Laraba.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Aiki Kan Rigakafin Covid -19
- Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Wannan gobara ta haddasa fashe-fashe da ƙara mai tsanani, wanda ya jefa jama’ar Maiduguri cikin tsoro.
Da dama daga cikin mazauna birnin sun yi zaton cewa Boko Haram ne suka kai hari.
Sai dai bayan bincike, hukumar kashe gobara ta ce gobarar na da alaƙa da tsananin zafin da ake fama da shi a Maiduguri.
Bayan gobarar, jami’an kashe gobara sun kai ɗauki, kuma sun samu nasarar kashe wutar.
A shekarar 2014, ƙungiyar Boko Haram ta kai wa wannan bariki na Giwa hari, inda ta kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp