Wani magidanci mai suna Muhammad Uba ɗan shekaru 67 da matarsa Fatima Muhammad mai shekaru 52 sun rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a Kano, biyo bayan wani lamari da ya faru ranar Juma’a a Rangaza, da ke unguwar Layin AU a ƙaramar hukumar Ungogo.
A cewar kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusif Abdullahi, dakin ikonsu ya samu kiran agajin gaggawa da misalin karfe 01:45 na dare daga ɗaya daga cikin ma’aikatansu FS Ahmad Abubakar.
- Gobara Ta Ƙone Kayayyakin Biliyoyin Naira A Rumbun Ajiya Na NSIPA Da Ke Abuja
- Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5
Ya ci gaba da bayanin cewa, tawagar da ke bakin aiki daga tashar kashe gobara ta Bompai, sun yi hanzarin zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka samu an yi nasarar shawo kan gobarar.
Ya ƙara da cewa ɗakuna biyu sun ƙone kurmus inda wani dattijo mai suna Muhammad Uba, da matarsa Fatima Muhammad, suka shaki hayaki sakamakon gobarar wanda bayan garzayawa da su asibiti aka tabbatar da mutuwarsu gabaɗaya.