Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar.
Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446.
Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin.
Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe.