Golan Real Madrid, Thibaut Courtois, ya samu rauni a gwiwarsa ta hagu, kuma da alama ba zai samu damar buga wasanni mafi yawa a kakar wasa ta bana ba.
Za a yi wa dan wasan na Belgium tiyata a kwanaki 31 masu zuwa.
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Soke “Doka Game Da Taiwan”
- Super Falcons Sun Dawo Gida Bayan Korarsu Daga Gasar Kofin Duniya
Courtois, wanda aka ba shi kyautar Gwarzon mai tsaron gida a duniya a kyautar Ballon d’Or a bara, ya lashe gasar La Liga ta Spain sau biyu tun da ya koma Real a 2018.
Ya buga wa Real wasanni 230, wacce za ta kara da Athletic Bilbao a wasansu na farko na gasar La Liga a ranar Asabar.
Courtois ya lashe gasar Premier sau biyu tare da Chelsea kafin ya koma Real a 2018.
Ya kuma lashe gasar zakarun Turai a 2022, inda ya nuna bajinta a wasan karshe da Liverpool.