Daga cikin abin da Manzon Allah (S.A.W) yake shagaltuwa da shi a goman ƙarshe na Ramadan akwai ittikafi (al-Li’itikaf). An karɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana ittikafi a goman ƙarshe na Ramadan” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Nana Aishatu Allah ya ƙara yarda a gare ta, ta ce: “Lalle Annabi (S.A.W) ya kasance yana ittikafi a goman ƙarshe na Ramadan har Allah ya karɓi rayuwarsa, sa’an nan matansa ma suka yi ittilafi a bayansa” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Manzon Allah (S.A.W) a ƙarahen rayuwarsa ya yi ittikafi na kwana 20 ne. Abu Huraira, Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: “Mamzon Allah (S.A.W) ya kasnace yana ittikafi na kwana goma a kowace shekara, amma a shekarar da ya yi wafati a cikinta sai ya yi ittikafi na kwana ashirin” Bukhari ne ya ruwaito.
Ya tabbata Annabi (S.A.W) ya taba yin ittikafi a goman ƙarshe na watan Shauwal da bai sami yinsa a Ramadan ba kamar yadda Bukhari da Muslim suka ruwaito.
Mene ne ittikafi?
Ittikafi a harshen Larabci yana nufin tsayuwa da dauwwama a kan wani abu. Saboda haka ne ma ake cewa da ya zauna kuma lazimci masallaci ‘Mu’utakifun da kuma Akifun.’ Domin ƙarin haske duba al-Faiyumi; Misbahul Munir [shafi na 219] da Ibnu al-Manzur; Lisanul Arab [9/252]
A shari’a ittikafi yana nufin wani mutum ya zauna ya lazimci masallaci a wata keɓantacciyar sifa ta daban” Ibnu Hajar; Fathul Bari [3/627].
Babban malamin Malikiyya al-Ƙarafi yana cewa: “Mutum ya tsare kansa a masallaci domin yin bauta ga Allah da wata keɓantacciyar sifa” al-Ƙarafi;¡ az-Zakhira [2/534].
Ittikafi yana daga cikin nafiloli da sunna ne aikata su. Duba Ibnu Abi Zaid al-Ƙairawani; ar-Risalatu [shafi na 88] da Khalil; Mukhtasar [shafi ma 105] da Ibnu Hajar Fathul Bari [4/627].