Gwamnatin Jihar Gombe da Gidauniyar ‘Bill and Melinda Gates’ (BMGF) sun jaddada aniyarsu ta samar da hadin gwiwa mai karfi da samar da muhimman dabaru don inganta bangarorin kiwon lafiya da noma.
An cimma wannar matsaya ce yayin wata muhimmiyar ganawa tsakanin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da tawagar gidauniyar ta BMGF, karkashin jagorancin Manajanta na Nijeriya, Mista Uche Amaonwu, a masaukin Gwamnan Gombe da ke Abuja.
- Trump Ya Gayyaci Mark Zuckerberg Cin Abinci
- Me Ya Sa Lee Hsien Loong Yake Da Karfin Gwiwa Kan Makomar Kasar Sin?
A yayin taron, Mista Amaonwu ya yaba wa Gwamna Inuwa bisa irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannonin kiwon lafiya, da ilimi, da sauransu, inda ya ce Jihar Gombe ta yi fice bisa tsare-tsarenta na kiwon lafiya masu inganci da nagarta.
Ya jaddada cewa an zabi Jihar Gombe a sabon shirin hadin gwiwa na gidauniyar ne saboda nagartattun tsare-tsarenta na kula da lafiya.
Ya kuma bayyana fatan cewa sabunta hadin gwiwar zai kara habaka ci gaba a fannin kiwon lafiya da bunkasa noma tare da samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar Jihar Gombe.
A nasa jawabin, Gwamna Inuwa ya bayyana wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun hawansa karagar mulki, inda ya bayyana cewa Jihar Gombe ta tashi daga mataki na kuran baya a fagen ci gaba zuwa mataki na gaba a fannonin tattalin arziki da zamantakewa.
Gwamnan ya jaddada fifikon da gwamnatinsa take bai wa fannin kiwon lafiya, ilimi, noma, da gina al’umma, wadanda duk suke da muhimmanci wajen samun ci gaba mai dorewa.
A bangaren kiwon lafiya, Gwamna Inuwa ya yi karin bayani kan wasu nasarorin da ya samu, ciki har da tabbatar da cewa dukkan gundumomi 114 da ke jihar suna da akalla cibiyar kiwon lafiya daya a matakin farko da kuma kafa hukumar taimakekeniyar lafiya ta Jihar Gombe (GoHealth), wacce ta dauki masu rauni da ke cin gajiyar jinya su fiye da 340,000.
Sauran nasarorin a cewarsa, sun hada da kafa hukumar kula da asibitoci don inganta harkokin kiwon lafiya, da gina sabin manya da kananan asibitoci a fadin jihar da daukar ma’aikatan lafiya aiki don magance gibin ma’aikata a fannin da dai sauransu.