Barkanku da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da yake ba wa kowa damar turo sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da sakonnin gaishe-gaishenku wadanda ku ka aiko mana da su, sai dai za mu karanto kadan ne daga cikin sakonnin da ku ka aiko mana duba da yanayin shafinmu na yau. Ga dai sakonnin kamar haka:
Sako daga Danlami Hadejia:
Ina gaishe da Ilu, Asabe, zainaba, Ishatu da Bilki, sannan ina gaisar Alh.Lukuman dan’isa, malam Haladu me turare, ina gaishe da matata Hadizatu da fatan za su yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Hamida Yusuf Jihar Kaduna:
Da farko ina yi wa daukacin al’unar musulmi barka da juna’a, sannan ina gaishe da mahaifiyata Haj. Asma’u da kuma mahaifina Alh. Yusif Gwani, ina gaida kawayena kamar su; Maryam, islam, da sauran kawayena na islamiyya.
Sako daga Fatima Yahaya Jihar Bauchi:
Ina mika sakon juma’a ta ga masoyina abun alfaharina uban ‘ya’yana kn sha Allah Al’amin, ina gaishe da kannen masoyina Ali, Ibrahim, Amina, Hamid, Fa’iza, ina fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Khalil Isah Muhammad Jihar Kano:
Ina gaishe da iyayena da abokaina kamar su; Ahmad dan gajere, Musbahu karkasara, Tahir, da kuma Zulyadaini Salis.
Sako daga Aisha Muhammad Birnin Kudu:
Dan Allah ina so a mika mun sakon gaisuwa ta zuwa ga Samira Muktar, da kuma Iklima Auwal da Jabir Usman, Ummy zee, da Kabir T.Y, fatan za su yi juma’a lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp