Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin GORON JUMA’A, shafin dake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga abokan arziki na kusa dana nesa. Kamar kowane mako shafin na tafe da sakonnin da ku ka aiko mana da su, inda sakon farko ya fara da cewa;
Sakon daga Yusuf Sa’id Gezawa Jihar Kano:
Ina gaishe da Mariya da Hajiya Ummu da Munira da Sayyada, sannan ina gaishe da Mahaifiyata ita ce farko Haj.Bilkisu da mahaifina Alh. Sa’eed Muhammad, ina fatan su yi juma’a lafiya.
Sako daga Saifullahi Adamu Jihar Jigawa:
Dan Allah Leadership ku mikan sakona zuwa ga Abdulyasar, da Hon. Ya’u da Malam Audu dan gora, da Safiya da Laure da kuma Malam Sabi’u Baba na kowa, sai Hajiya Bebi me sakwarar ‘yan gayu, da dukkanin ‘yan majalisar mu ina yi musu fatan alkairi.
Sako daga Halima Nasir Kaduna:
Ina so a mikan sakonaisuwa zuwa ga kawayena kamar su; Aisha, Laila, Maryam’s Kitchen, Zuby, Halisa ‘yar dagwas, Zuzu da Teemah. Sannan ina gaida kannena irin su; Al’amin, Muktar, Rashida da Rukayya.
Sako daga Fatima Ibrahim:
Ina gaishe da masoyina abin kaunata kuma rabin raina Mahir Mamuda (M2), sai kannena da kuma sauran ‘yan’uwana ina addu’ar Allah ya sa su yi juma’a lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp