Jama’a barkanku da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.
A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gaishe-gaishen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkanin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman editana Abdulrazak Yahuza Jere, da sauran al’ummar musulmi baki daya, da fatan an yi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a tare da kai ziyara lafiya. Yanzu kuma zan je ga sakonnin masu karatu kamar haka:
Sako daga Habib Ahmad Jihar Kano Unguwar Goron Dutse:
Ina gaida ‘Yan uwana da ke garin Jos, irinsu Maryamu, Ummussalama, khadijatu, Auwal, Isuhu da sauransu. Sannan ina gaida Malamina Malam Muttaka da kuma Baballe abokina, ina gaida ‘Yan kungiyarmu ta ball, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Assalamualaiku sunana HABIBU ABDULRAZAK ZANGONDAURA. Ina Mika sakon barka da Juma’a ga dukkanin Al’ummar da ke fadin duniya.
08136968743
Sako daga Usman Bello Jihar Katsina:
Ina gaida Hajiyata, Mamana kenan Haj. Karima, kowa ya bar gida, gida ya barshi, sai mahaifina Alh. Bello, sai kannena da abokaina, irinsu, Yahaya ikon Allah, su Idris Shettima, Dan Maraya Musa, Lukman a zauna lafiya, ina gaida matata Hafsat Bebin bebi, ina gaida ‘Yan uwanta da kannenta gaba daya, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako Daga Yusif Umar Wudil 08067265187
Assalamu alaikum, ina mai muku fatan alkhairi Allah ya kara daga darajar wannan gidan jarida da maaikatansa amin. Da farko dai ina mai mika gaisuwata zuwa ga iyayena da ‘yan’uwana maza da mata sannan kuma ina gaida babban abokina wato Ibrahim Sani Wudil.
Sako daga Al’amin Shehu Dan Gaske Jihar Kaduna:
Assalam. Ina gaida Mahaifana, ina gaida sauran ‘Yan uwana, da abokan karatuna wadanda na juma ban gansu ba, da wadanda ma muke haduwa har yanzu, ina gaida Ummi da Mami, da Fati, ina gaida Abdulkareem, Idris dan baiwa, ina gaida, Alhaji Ali mazan duniya, ina gaida sauran al’umma gaba daya da fatan kowa yayi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08164205067, 08127909054:
Ass. Gaisuwar Goron Juma’a zuwa ga mai girma tsohon shugaban hukumar DSS, na kasa Alh. Lawal Musa Daura, da Alh.Sani Musa da shugaban karamar hukumar Daura, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Gimbiya Aishat Sa’id Jihar Bauchi:
Gaisuwar goron juma’a zuwa ga ‘yan uwa musulmi, da fatan sun yi juma’a lafiya. Ina gaida Zakiya da Haj.Mero, da Haj. Marka, da Haj. Sa’adatu me tuwon shinkafa, ina gaida Maryamu Isah, ina gaida Dijen Malan Aminu, da Hidayatu Ibrahim, ina gaida Abubakar Mustapha, Arabian kingboi, Muhd Kalgo, Mika’il Adam, da sauransu. Da fatan kowa yayi Juma’a lafiya.