Jama’a barkanmu da shigowa wata mai girma, wata mai alfamar wato watan ramadana, yadda muka fara wannan azumi lafiya, Allah ubangiji ya sa mu gama lafiya, ya kuma ba mu dukkanin ladan da ke cikin wannan wata mai alfarma na ramadan, Allah ya yafe mana kurakuranmu amin.
Barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa.
Kafin na fara mika sakonnin da ku ka aiko mana sai na fara mika tawa gaisuwar zuwa ga Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan za ka kammala azumi lafiya, kuma za ka sha ruwa lafiya, tare da sallar juma’a lafiya.
Sakon gaisuwar goron juma’a na gaba zuwa ga mataimakin Edita Hamza Bello da fatan za ka kammala azumi lafiya, sako na gaba zuwa ga Khalid Idris Doya da fatan kai ma za ka kammala azumi lafiya.
  Gaisuwa da fatan alkhairi na goron juma’a zuwa ga Bilkisu Tijjani da sauran ma’aikata baki daya wadanda ban zayyano ba, da fatan kowa zai kammala azumi lafiya, kuma za a sha ruwa lafiya.
Yanzu kuma zan je ga sakonnin masu karatu kamar haka:
Sako daga Jafar Mu’azu kwanar dan gora:
Ina mika sakon goron juma’a zuwa ga Lami me sakwara, da Hajiya Abu, da Hajiya Lauratu mai adashi, ina gaida yarinta Bintu, da Asabe da mardiyya, Allah ya sa za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Abdullahi Yahaya Rijiyar Lemo Jihar Kano:
Ina gaida sahibata abar kaunata Zainab Kabir, da kuma kannenta Aisha da Maryama da kuma Auwal, ina gaida mahaifiyata Hadiza Isma’il da babana Alhaji Yahaya mai atamfa, ina gaida abokaina wadanda muke tare da su, da wadanda ba ma tare a yanzu ina gaishe su a duk inda suke, da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Rahinatu Idris (‘Yar Mala) Jihar Kaduna:
Ina gaida kawayena kamar su; Hajara, Latifa, maimuna, baby ‘yar mama, sadiya Abdulrahman, Hauwa’u Abba, fiddausi dada sauransu, ina yi musu addu’a su sha ruwa lafiya. Sannan ina gaida Ummana Hajiya Momi da Abbana Alhaji Idris da kuma kannena da yayyena, Allah ya ba mu wucewa lafiya na wannan wata.
Sako daga Safiya Ibrahim Jihar Jos:
Ina gaida Habibi mai sunan ‘yan gayu Nasir Bashir Ahmad, masoyina in sha Allah, ina gaida Antis di na Anti Farida, da Anti Maryam, da Anti Jamila, da Anti Ummi, ina gaida kanwata rigimammiya ‘yar autan Momi Hafsat da sauran kannena, da fatan za su sha ruwa lafiya.
Sako daga Aliyu Salis Jihar Kano:
Ina gaida al’ummar musulmi bakidaya na fadin duniya, ina kuma yi wa kowa addu’ar Allah ya kawo mana mafita cikin hakin da ake ciki na tsanani, ina kuma addu’a wannan wata da muke ciki Allah ya sa kowa ya gama azumi kafiya, ina gaishe da kowa na gidanmu tun daga kan mahaifana har zuwa kn yayyena da kannena da kuma abokanaina, Allah ya ba mu ladan wannan rana ta juma’a.
Sako daga Fati Tijjani:
Assalaikum alaikum! Al’umar musulmi baki daya, ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na mamana da babana ina musu fatan alkhairi da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana kannena da fatan sunyi sallar juma’a lafiya. Ina gaida kannan mamana da kannan babana tare da yi musu fatan anyi sallar juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da juma’a.
Sako daga Alkazim Garba,
Ina mika sakon gaisuwa da goron jumma’ah ga aboki na Musa Bale da yake Wuse Zone 6, yayana Mahdi da ke nan Wuse Zone 6, yayana Ishak da matar sa Hanifa da ke dawaki.
Sako daga Amina Aliyu
Ina mika sakon gaisuwa da goron jumma’ah ga abokiya ta Hassana zakari da take life camp, yayata Fatima da ke nan Apo, yayana Muhammad da matar sa Rukayya da ke Asokoro