Jama’a barkanmu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.
A yau ma ina yi dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
Sako daga Fatima Aliyu
Assalamu alaikum!
Ina yi mika godiyata ga ma’aikatan gidan wannan jarida mai albarka tare da sakon gaisuwata da suka bani dama da na mika sakon gaisuwata na gode.
Ina yi mika sakon gaisuwata ga iyayena da yayyena da kannena ‘yan uwana mata da maza wadanda muka yi makaranta tare da ku, al’ummar Musulmi baki daya duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi mishi fatan alkhairi da fatan an yi Sallah Juma’a lafiya.
Sako daga Abubakar Tijjani:
Assalaikum alaikum!
Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannensu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Rabi’u Aliyu
Ina yi mika sakon Goron Juma’a ga al’ummar Musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro dake kasar nan baki daya. Ina mika gaisuwata ga mahaifiyata Hajiya Lamee Musa, da mahaifina Alhaji Aliyu Isah. Ina yi mika sakon gaisuwa na ga yayata Ummi, da kanwata Aisha, da yayana faisal, da kanina Abdulrahman, da yayana sadik. Da fatan sako na ya iso ku cikin koshi. Lafiya.
Sako daga Zaina Bello
Ina yi mika sakon gaisuwata zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana amin ya Allah.
Sako daga Maimuma Muhammad
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na LEADERSHIP HAUSA tare da mika godiya ta da suka bani dama da na mika sakon gasuwata na gode.
Ina yi mika sakon gaisuwa ta ga mijina yi da iyaye na ina yi fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina yi mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan ‘uwana yayyena da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Asma’u Usman
Assalamu alaikum! Ina yi mika sako gaisuwata ga mutanen gidan wannan jarida mai albarka tare da mika godiya ta da suka bani dama da na mika sakon gaisuwata na gida.
Ina gaida Iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki, abokan karatu da abokan aiki na da al’ummar Musulmi baki daya tare da barka da Juma’a da fatan an yi Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.